• Leadership Hausa
Wednesday, February 8, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

IMMOWA Ta Horar Da Mata Da Yaran Jami’an Shige Da Fice Sana’o’i  

by Yusuf Shuaibu
5 months ago
in Labarai
0
IMMOWA

Ƙungiyar matan jami’an hukumar shige da fice ta ƙasa (IMMOWA) ta horar da mata da yara sana’o’in dogaro da kai.

Ƙungiyar ta yi bikin bai wa waɗanda suka samu horon takardun shaida a shalkwatan hukumar ta NIS da ke Abuja.

  • An Kama Mai Shiga Tsakanin Iyalai Da Masu Garkuwar Jirgin Kasan Kaduna A Masar

Da take gabatar da jawabi lokacin bikin, Uwargidan shugaban hukumar shige da fita ta ƙasa, Hajiya Maryam Isah Jere ta nuna jin daɗinta bisa samun nasarar horar da mata da yara sana’o’in dogaro da kai tare da ɗora yara a tafarkin tarbiya.

Shugabar ƙungiyar ta ja kunnen waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da abubuwan da suka koya wajen tallafa wa kansu da kuma al’umma gaba ɗaya.

“Ina ƙara wa waɗanda suka amfana da wannan horo ƙwarin gwiwa da su ci gaba da gudanar da sana’o’in da suka koya wajen inganta rayuwarsu.

Labarai Masu Nasaba

CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023

Malamin Islamiyya Ya Shiga Hannun Hukumar Hisbah Kan Lalata Da Dalibansa A Kano

“Haka kuma ina jinjina ga dukkan waɗanda suka taimaka har aka samu nasarar gudanar da wannan horo. Wannan shirin yana bunƙasa ƙungiyar IMMOWA, wanda yake samun tallafi daga wurin maigidana da sauran jami’ai da ke ƙoƙarin bunƙasa rayuwar mata da yara,” in ji Hajiya Maryam.

Shugabar IMMOWA ta ƙara da cewa maƙasudin wannan shirin shi ne, saboda rashin tsaro da ake fama da shi wanda ya sa yara suna zaune a gida lokacin da iyayansu suke wuraren aiki. Ta ce sun yi tunanin haɗa yaran wuri ɗaya lokacin da iyayensu suke ofis, domin su koyi sana’o’in dogaro da kai.

A cewarta, ta gamsu da irin sakamakon da shirin ya bayar, domin tana ɗaya daga cikin waɗanda suke halartar horon a ko da yaushe tare da mambobin ƙugiyar IMMOWA.

Ta ce wasu daga cikin iyayen yaran suna kiran ta a waya domin nuna godiya da irin tarbiyar da yaran suka samu, inda suka ce a baya yaran ba sa iya gaida kansu, amma a yanzu suna yi. “Sai dai kuma ni ba na buƙatar godiyar mutane, ina neman lada daga wurin Allah.”

Shi ma da yake jawabi, Shugaban hukumar NIS, Isah Idris Jere ya bayyana cewa shirin ƙungiyar IMMOWA ya zo a kan gaɓa ta yadda zai bunƙasa rayuwar jami’ai mata da yaransu.

Wanda ɗaya daga cikin manyan mataimakansa, DCG Dupe Anyalechi ta wakilta a taron, CGI Isah Jere ya ce ƙungiyar ta sauya akalar matan jami’an hukumar ta yadda za su taimaka wa iyalansu da kuma al’umma gaba ɗaya daga abin da suka koya.

Ƙungiyar ta horar da mata da yara yadda ake haɗa sabulu da jaka da burodi da kek da dai sauran kayayyaki da ake amfani da su na yau da kullun.

Previous Post

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Kenya

Next Post

NIS Da NDLEA Reshen Bayelsa Sun Yi Ƙawancen Fatattakar Miyagun Ƙwayoyi Da Baƙin Haure

Related

CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023
Labarai

CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023

3 hours ago
Malamin Islamiyya Ya Shiga Hannun Hukumar Hisbah Kan Lalata Da Dalibansa A Kano
Labarai

Malamin Islamiyya Ya Shiga Hannun Hukumar Hisbah Kan Lalata Da Dalibansa A Kano

3 hours ago
Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari
Labarai

Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari

5 hours ago
Sauyin Kudi: Buhari Ya Gana Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Da Emefiele
Labarai

Sauyin Kudi: Buhari Ya Gana Da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Da Emefiele

7 hours ago
Babu Dan Nijeriya Da Girgizar Kasar Turkiyya Ta Shafa – Jakada
Manyan Labarai

Babu Dan Nijeriya Da Girgizar Kasar Turkiyya Ta Shafa – Jakada

10 hours ago
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Daya, Sun Sace 10 A Jihar Neja
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Daya, Sun Sace 10 A Jihar Neja

10 hours ago
Next Post
NDLEA

NIS Da NDLEA Reshen Bayelsa Sun Yi Ƙawancen Fatattakar Miyagun Ƙwayoyi Da Baƙin Haure

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kai Zuciya Nesa Game Da Batun Kumbon Farar Hula Da Ta Harbo

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Kai Zuciya Nesa Game Da Batun Kumbon Farar Hula Da Ta Harbo

February 7, 2023
Zan Tabbatar Da An Ci Gajiyar Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe Muddin Aka Zabe Ni – Atiku

Zan Tabbatar Da An Ci Gajiyar Man Fetur A Yankin Bauchi Da Gombe Muddin Aka Zabe Ni – Atiku

February 7, 2023
Masana’antun Kasar Sin Sun Taka Rawa Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya

Masana’antun Kasar Sin Sun Taka Rawa Wajen Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya

February 7, 2023
Gwajin Dawo Da Rukunonin Yawon Bude Ido Zuwa Kasashen Ketare Da Sin Ke Yi Zai Farfado Da Kasuwar Yawon Bude Ido Ta Duniya

Gwajin Dawo Da Rukunonin Yawon Bude Ido Zuwa Kasashen Ketare Da Sin Ke Yi Zai Farfado Da Kasuwar Yawon Bude Ido Ta Duniya

February 7, 2023
Kungiyar Ibo A Jihar Kaduna Ta Nuna Goyon Bayan Ga Sanata Uba Sani

Kungiyar Ibo A Jihar Kaduna Ta Nuna Goyon Bayan Ga Sanata Uba Sani

February 7, 2023
CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023

CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023

February 7, 2023
Sin Ta Kaddamar Da Tsarin Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Türkiyya Da Syria

Sin Ta Kaddamar Da Tsarin Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Türkiyya Da Syria

February 7, 2023
Malamin Islamiyya Ya Shiga Hannun Hukumar Hisbah Kan Lalata Da Dalibansa A Kano

Malamin Islamiyya Ya Shiga Hannun Hukumar Hisbah Kan Lalata Da Dalibansa A Kano

February 7, 2023
Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Fahimta Da Aiwatar Da Matakan Ingiza Zamanintarwa Iri Na Kasar Sin

Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Fahimta Da Aiwatar Da Matakan Ingiza Zamanintarwa Iri Na Kasar Sin

February 7, 2023
Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari

Sauyin Kudi: Bankin Zenith Ya Rufe Wasu Rassansa A Nijeriya Sakamakon Kai Masa Hari

February 7, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.