Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya gudanar da taron tattaunawa da jami’an da ba ‘yan jam’iyyar ba, a Zhongnanhai dake birnin Beijing a baya bayan nan.
Taron ya nemi jin ra’ayoyi da shawarwari daga shugabannin kwamitin kolin jam’iyyun demokuradiyya daban-daban, da shugabannin hukumomin masana’antu da cinikayya na kasar Sin, da kuma wakilan jama’ar da ba sa cikin kowace jam’iyya, game da yanayin tattalin arzikin kasar a bana da kuma ayyukan raya shi a shekara mai zuwa.
Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ne ya jagoranci taron, kuma cikin jawabin da ya gabatar, ya jadadda cewa, muradun dake sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin Sin cikin dogon lokaci ba su canza ba, dole ne a karfafa gwiwa, da amfani da fa’idojin da ake da su, da kuma shawo kan kalubale, kana a ci gaba da ingantawa da fadada ci gaban tattalin arzikin cikin kwanciyar hankali, ta yadda za a samu kyakkyawan mafari yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15.
Xi Jinping ya bayyana cewa, za a gudanar da ayyukan tattalin arziki na shekara mai zuwa yadda ya kamata, kuma ya kamata a bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko bisa yanayin sassan kasar, da inganta gina kasuwar kasa mai hadin kai, da ci gaba da rigakafi da kuma maganin hadari a muhimman fannoni, da kiyaye jituwa da kwanciyar hankalin al’umma. (Safiyah Ma)














