Sojojin runduna ta 6, na sashe na 3 ‘Operation Whirl Stroke’, sun yi nasarar dakile harin fashi da makami, inda suka ceto wadanda aka sace, sannan suka kwato makamai a cikin jerin ayyukan bincike da rundunar ke yi fadin jihar Taraba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Laftanar Umar Muhammad, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, ya ce sojojin sun amsa kiran gaggawa a ranar 6 ga Disamba bayan da ‘yan fashi da makami suka toshe hanyar Manya-Takum, suka tare matafiya.
- Kwamitin Kolin JKS Ya Saurari Shawarwarin Jami’an Da Ba ‘Yan Jam’iyyar Ba Game Da Ayyukan Raya Tattalin Arziki
- Bukola Saraki Ya Je Bauchi Ta’aziyyar Ɗahiru Bauchi
“Sojojin sun yi gaggawar hallara wurin inda suka tarwatsa ‘yan fashin, inda suka gudu cikin firgici suka bar wasu makamansu.
“Binciken da aka gudanar na bin sahun ‘yan fashin, an gano bindiga kirar AK-47 guda 1, mujallar AK-47 guda 1, da harsasai,” in ji sanarwar.














