Ofishin siyasa kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin ya kira taro a yau Litinin, domin nazarin ayyukan tattalin arziki na shekarar 2026, da kuma duba “Ayar doka ta tafiyar da harkokin kasar Sin bisa doka karkashin shugabancin jami’iyyar JKS a dukkan fannoni”. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya jagoranci taron.
Taron ya yi imanin cewa, bana shekara ce mai muhimmanci a fannin zamanintar da al’ummar Sinawa, inda tattalin arzikin kasar yake tafiya ba tare da tangarda ba, kana sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko na ci gaba da bunkasa, kuma ayyukan kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje na ci gaba da karfafa. A daya bangaren kuma, an samu ci gaba mai kyau wajen warware hadurran da ke cikin muhimman fagage, kana an kara karfafa tabbacin rayuwar jama’a, kuma an ci gaba da bunkasa zaman lafiya a cikin al’umma.
Taron ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da raya ayyukan tattalin arziki mai inganci na shekara mai zuwa cikin kwanciyar hankali, da kuma ci gaba da aiwatar da manufofin kasafi masu karko da bude bakin aljihu, don tabbatar da ingantaccen tsarin tattalin arzikin kasa daga manyan fannoni.
Taron ya kuma bayyana cewa, kafa “Ayar doka ta tafiyar da harkokin kasar Sin bisa doka karkashin shugabancin jami’iyyar JKS a dukkan fannoni”, na da muhimmanci sosai wajen kara karfin jam’iyyar a fannin gudanar da harkokin kasa a bangarorin kimiyya, da tsare-tsare, ta yadda za a kafa cikakken tsarin doka na gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, da kuma gina kasa mafi karfin gudanar da harkoki bisa doka. (Amina Xu)














