Cibiyar da ke shirya bita da wayar da kan al’uma kan fasahar sadarwa ta zamani (CITAD) tare da hadin guiwar cibiyar (Hope Action Progress), sun shirya wani taron bita da wayar da kan mata da matasa a Kano kan sha’anin mulki da siyasa da yadda ake gudanar da mulki da hulda da Jama’a.
Cibiyar ta gudanar da taron ranar Litinin a Otel din Tahir da ke Kano, ta kuma bayyana cewa ce a baya ta gudanar da irin wadannan bitoci ga mata da matasa don su fahimci muhimmancin shiga cikin harkokin mulki da sha’anin siyasa a dama da su wurin neman madafun iko.
- Burinmu Mata Da Matasa Su Fito A Dama Da Su A Harkokin Mulki Da Siyasa — CITAD
- Ana Rade-Radin APC Ta Tsayar Da Ahmad Lawan A Matsayin Dan Takarar Masalaha
Babbar daraktar shirye-shirye a cibiyar (AAN) kuma guda cikin masu gabatar da kasidu a taron, Suwaiba Muhammad Dankabo, ta bayyana cewa, idan zaka shiga cikin harkokin siyasa kana mai goyan baya ko kuma tsaya wa ka yi a zabe ka, kana da bukatar sanin wasu muhimman al’amura.
Dankabo, ta ce wannan dalilin ne ma yasa suka shirya bita don ilimantar da mata da matasa idan sun samu mulki su san yadda za su tafiyar da shi da yadda za su yi mu’amala da Jama’a.
Da aka tambaye ta shin yanzu kwalliya na biyan kudin sabulu a irin wadannan taruka da suke shirya wa, sai ta kayara da baki ta ce,” Tabbas kwalliya ta fara biyan kudin sabulu don kuwa mun zauna da shugabannin Jam’iyyu a baya kan su ba mata da matasa damar shiga a dama da su a sha’anin mulki da siyasa, suma su tsaya takara a zabe su,”
“Yanzu haka wasu Jam’iyyun sun amsa wannan kiran namu don ko Jam’iyyar PRP a kasa ta ba kaso mai tsoka a matakai daban-daban a takara, haka takwararta Jam’iyyar YPP ta ba mata da matasa akalla 70 tikitin takara, ita ma Jam’iyyar PDP ta ba mata biyu damar tsayawa takara,” in ji Suwaiba.
“Babban Kudurinmu shi ne, a bawa mata da matasa damar su fito su tsaya takara kuma a zabe su a madafun iko daban-daban a Nijeriya ta yadda za su samar da aiyukan yi da tsakulo matsalolin al’uma da magance su, saboda mutumin da yake da damar mulki ya fi kowa kwazon kawo sauyi a cikin al’uma.” A Cewar Dankabo.
A nasa jawabin shugaban Jam’iyyar PRP na Jihar Kano, Abba Sule Namatazu, ya ce Jam’iyyarsu ta PRO tuni ta amsa wannan kiran don kuwa sun ba matasa kaso 75 cikin 100 damar tsayawa takara a kujeru daban-dabn kuma dan takararsu na Kano ma matashi ne mai karancin shekaru, kuma sun ba mata biyu kujerar wakilci a tarayya