‘Yan Nijeriya musanmman ‘yan asalin yankin arewa na cigaba da yin fice a harkokin bunkasa rayuwar al’umma a sassan Duniya, ta baya-bayan nan ita ce, wata ‘yan asaloin Jihar Kano a Arewacin Nijeriya mai suna Munayah Yusuf Hassan wadda ta samu nasarar zama Mai Shari’a tare da kuma da gabatar da kara a Manyan Kotunan kasar Ingila da yankin Wales.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani shahafrraen Lauya mai zaman kansa kuma mai fafutukar kare hakkin al’umma a Nijeriya mai suna Bulama Bukarti.
- ‘Muna Kira A Samar Da Jami’an Tsaro Na Yankin Arewacin Nijeriya’
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Bayanin da LEADERSHIP Hausa ta samu ya nuna cewa, Munayah ta kammala digirinta na farko ne a fannin aikin lauya daga Jami’ar Bayero da ke Kano, ta kuma halarci Babban Makarantar Lauyoyi don kwarewa tare da zama cikakkiyar lauya a Nijeriya kafin daga nan ta koma kasa Birtaniya tare da mijinta wani kwarren mai ilimin zane-zane, don cigaba da rayuwa.
Daga nan ne ta shiga harkokin ta na shari’a a kotunan kasar Birtaniya inda har hukumar shari’ar kasar ta gano irin kwazon ta aka kuma nada a wannan matsayiin.
A mastayinta na mai shari’a a manyan kotunan Birtaniya da Wales, cikin aikinta shi ne shiryarwa tare da bayar da shawara ga masu shari’a da masu neman kariya a yayin da suke fuskantar shari’a a yankin na Birtaniya da Wales gaba daya.
Suna kuma shiga tare da warware harkokin shari’a da suka hada da na kasuwanci, manyan laifukka, rikicerikice da suka shafi iyali da matsalolin yau da kullun a tsakanin al’umma.
A ranar Litinin ne aka kaddamar da Munayah a wata kayatacciyar biki da aka yi a Ingila inda ta ta yi rantsuwar yin aiki tukuru kamar yadda kundin tsarin mulkin Birtaniya ya samar ba tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba.
Munayah ta zama abin alfahari ga dukkan al’umma yankin arewacin Nijeriya musamman ganin ita ce mace ta farko da ta fara rike wannan matsayi na mai shari’a a manyan kotunan kasar Birtaniya, wannan na kuma zuwa ne a lokacin da ake ganin matan arewa a matsayin wadanda ke koma baya a fannin ilimi da harkokin cigaban al’umma.
Wannan nasara da Munayah ta samu kuma zai kara zaburar da mata da samari ‘yan arewa don su kara kaimin fuskantar karatukan su a fannoni da dama don suma su kai ga kololiyar nasara a bangaren da suka zaba wa kansu a duk inda suka samu kansu a fadin duniyar nan.
A tattanawar da ta yi da manema labarai bayan an rantsar da iya, Munayah Yusuf Hassan ta mika godiya ga Allah a bisa wannan nasarar da ta samu ta kuma gode wa mijinta da sauran ‘yan uwa a kan irin goyon bayan da suka bata a dukkan lokutta har ta kai ga samun wannan nasarar.
Muna addu’ar Allah ya sa wannan ya zama sanadiyyar daukaka ga Munayah, ‘yanuwa da abokan arzikinta da al’ummar yankin arewa dama Nijeriya gaba daya, da fatan kuma zai zama wani matakala na daukaka da abin koyi ga matasanmu na yankin Arewa don su kara kaimi a harkokin su na rayuwa daban-daban.