Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta samu nasarar damke wasu mutum 19 da ake zargin ‘yan fashi da makani ne da suka addabi jihar.
Rundunar ‘yansandan ta yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen dakile matsalar tsaro a jihar.
- Za A Sanya Wa Kamfanonin Jiragen Sama Da Ke Sayar Tikiti Da Dala Takunkumi
- Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara Ta Mayar Wa Alhazai 1,318 Naira 50,000 Kowanne
Kwamishinan ‘yan sanda jihar, Dauda Idris Dabban shi ya yi wannan kira a shalkwatan ‘yan sanda lokacin gabatar da wasu mutane sha tara (19) da ake zargi da aikata fashi da makami.
Haka kuma, ya bayyana cewar daga cikin wadanda ake zargin akwai mutane 13 da ake zargi da satar motoci.
Kwamishinn ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin suke da alhakkin aikata mafi yawancin ayyukan fashi da makami musamman a cikin birnin Katsina.
Jagoran gungun wadanda ake zargi da fashi da makamin, Muhammad Ibrahim Lawal wanda aka fi sani da Abba Kala an damka shi tare da wata motar da ake zargi ya sace.
An dai damke wasu da ake zargin ne a jihohin Jigawa, Kano da kuma Jos suna kokarin guduwa da motocin da suka sata.
Dabban ya gode wa gwamnatin Jihar Katsina bisa taimaka wa hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu daidai da yadda doka ta tanada.