Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai mai kula da harkokin ilimin bai-daya, UBEC a ranar Talata ya gargadi gwamnonin kasar nan da su ba da fifiko ga ilimin firamare ko kuma su kasance a shirye kan sakamakon da zai biyo baya.
Shugaban kwamitin Farfesa Julius Ihonvbere ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar Kwara a karshen ziyarar kwanaki biyu da suka kai domin duba ayyukan UBEC-SUBEB da aka kammala a jihar.
A cewarsa, “Ina so in ba gwamnatocin jihohi shawara da su dauki matakin ilimi da muhimmanci domin amfanin kansu.
“Motoci masu hana harsashi, karnuka da manyan katangu ba za su iya ceton su daga fushin yaran da ba su sami damar yin karatu ba, don cin zarafi da wariya”.
Ya ce ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta jihohin da aka samu sun karkatar da tallafin da hukumar kula da Ilimin bai-daya (UBEC) ke bai wa Jihohi ba.