Jiga-jigai biyu na jam’iyyar APC, Hon. Yakubu Dogara (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin ta Tarayya) da Babachir David Lawal (Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya) na ci gaba da nuna adawarsu da matakin da jam’iyyar APC ta dauka na yin tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.
Inda suka ce yakin da suke yi suna yi ne domin neman adalci kuma za su cigaba da yin hakan.
Yakubu Dogara ya sanar da hakan ne bayan wata ganawar da suka yi da shugabannin Kiristoci daga jihohi 19 na arewacin kasar nan da kuma babban birnin tarayya a ranar Talata.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, APC ta zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takararta shugaban kasa a yayin zaben 2023, inda shi kuma ya zabo tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa kuma dukkaninsu musulmai ne.
Matakin da ke samun suka da adawa daga wasu Kiristoci na jam’iyyar APC har zuwa yanzu.
Dogara ya wallafa a shafinsa na Tuwita da Facebook a ranar Talata cewa, ganawar da suka yi da shugabannin Kiristoci daga jihohin arewa da FCT sun yi ne domin tattauna matakin da za su dauka kan zaben 2023 da ke tafe.
Ya wallafa da cewa, “ZabenNijeriya2023: Yakin neman adalci na cigaba da gudana. A yau, mun gudanar da ganawa ta neman shawarori da shugabannin Kiristoci na jihohin arewa 19 da kuma birnin tarayya Abuja domin tattauna batutuwan da suka shafi zaben 2023 kan wacce jam’iyya ce ta dace mu amince da ita a zaben 2023.”
Wakilinmu ya labarto cewa tun bayan da APC da ki daukan matakin canza ‘yan takarar musulmai biyu ake ganin su Dogara da Babachir ka iya kin goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyar a zaben 2023 da yiyuwar ma su mara wa wata jam’iyyar baya a tsakanin PDP, NNPP ko LP.