Mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da ‘yan ta’adda suka kai farmaki tare da tarwatsa jama’a a garuruwa 21 a Karamar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato.
Shugaban Karamar Hukumar, Honarabul Lawali Marafa Fakku, a yayin da yake tabbatar da harin ‘yan ta’addan a jiya Talata ya bayyana cewar sama da garuruwa 21 ne a mazabu uku cikin goma ‘yan bindigar suka kai farmaki tare da tarwatsa al’umma.
Ya ce ‘yan ta’addan sun fito ne daga makwabtan Jihohin Zamfara, Kebbi da Neja. “Sun gudu ne daga wadannan makwabtan Jihohin a bisa ga zafin hare- haren da jami’an soji ke kai masu, don haka suka zabi dawowa a nan a matsayin mafakar da ba ta da illa.” Ya bayyana.
Ya bayyana cewar a yanzu haka al’ummar yankunan na ci-gaba da binciken gawarwakin ‘yan uwansu da maharan suka yi wa kisan gilla a wuraren da aka kai hare-haren.
Shugaban Karamar Hukumar ya kum bayyana cewar an fara kai hare- haren ne a ranar Alhamis din makon jiya tare da rokon Gwamnatin Tarayya da ta kawo masu dauki ta hanyar farmakin sojoji kamar yadda aka yi a yankin shekaru uku da suka gabata.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato, Sanusi Abubakar ya bayyana cewar Rundunarsa ta na sane da hare- haren na ‘yan ta’adda haka ma tuni sun tura jami’ansu na musamman a Karamar Hukumar domin kai masu dauki.