A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bimillahir rahmanir Rahim. Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal-khatimi lima sabaka nasiril hakki bil-hakki wal-hadi ila siradikal mustakimi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim.
Wa radiyallahu an As’habi Rasulillahi (SAW), wa la haula wa la kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya himmatas shaikh ihdiri lana bi hazhal mahdari wal-ta’adifi bi nazaritin ta’ati lana bizzafari.
Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Idan ba a manta ba a makon da ya gabata muna ci gaba darasi ne a kan sabuwar shekarar Hijrah. Za mu kwana a inda muka tsaya a makon da ya gabata, sai kuma Allah ya kai mu lokacin da karatun yake da munasaba.
Cikin yardar Allah za mu dora darasinmu da muke yi a kan Shugaban Kaunu gaba daya, Annabi Muhammadu (SAW). Idan za a iya tunawa, mun katse karatun a lokacin da Ramadan ya gabato domin gabatar da darasi a kan azumi. Bayan Sallah kuma muka dora da bayani a kan Aikin Hajji har dai zuwa sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira ta 1444 wanda muka dakatar kamar yadda muka fada a baya.
Alhamdu lillah, yanzu za mu dora daga inda muka tsaya a wancan lokacin inda za mu dan yi waiwaye kadan dangane da daukakar nasabarsa da girman wurin da ya taso (SAW).
Yana daga cikin abin da ba a bukatar a kafa dalili a kansa, in dai kai musulmi ne ba ka bukatar sai an gaya maka daukakar nasaba, dangi da girman garinsa da girman inda ya taso (SAW), ko ka ce akwai wani bayani mai rikitarwa da sai an maka bayaninsu, ko akwai wani abu boyayye a ciki, shi Annabi (SAW) zababben Bani Hashim ne, ta bangaren kyau, iya magana, Ilimi da dukkan alheri, haka aka san ‘ya’yan Hashimu da wadannan kyawawan halitta.
Ya ishe mu alfahari cewa duk kyawun Abdulmuddalibi, shi ne shugaban Bani Hashim amma gashi yana wa Annabi waka yana cewa “Wa Ab’yadu yustaskal gamamu bi wajhihi, simalul yatama ismatun lil aramili – fari ne wanda da albarkar fuskarsa ake shayar da girgije, Uban marasa Uba kuma mijin mata gwagware.
“Takdi bihin nakatul ajma’u mu’utajiran bil burdikal badri jalla lailataz zulami – rakumi yanayin taku daidai da shi, ya lulluba da bargo kai ka ce wata ne da ya bayyana a cikin dare mai duhu.
“Yaluzu bihil hullaku min ali Hashimin, wahum indahum fi ni’imatin wa fawadili – Halakakkun Bani Hashim da shi suke fakewa, kuma shi (Annabi SAW) mai ni’ima ne da babbar daraja a wajensu”
Shi ne zababben Bani Hashim, haifaffen Bani Hashim, shi ne mafi daukakan Larabawa kuma mafi buwayarsu ta dukkan bangare na Mahaifinsa da bangaren mahaifiyarsa duk babu kamarsa sannan kuma dan garin Makkah ne wacce ita ce mafi girman garuruwan Allah da wajen bayin Allah.
Alkalin Alkalai ya yi mana Hadisi, Hussaini bin Muhammadus Sadafiyyu (Allah Ya rahamshe shi) ya ruwaito Hadisi inda ya daga Salsalar hadisin har zuwa Abu Hurairata daga Annabi (SAW) ya ce: “Bu’istu min kairi kuruni bani Adama, karnan fa karnan, hatta kuntu minal karnillazi kuntu fihi – An tashe ni daga fiyayyen zamaninnikan ‘yan Adam, tsara bayan tsara, tun daga zamanin Annabi Adam har na zo cikin wannan zamanin da nake ciki”
An karba daga Abbas bin Abdulmuddalibi ya ce, Annabi (SAW) ya ce “ Innallaha Ta’ala khalakal khalka waja’alani min kairim, min kairi karnihim, summa takhayyaral kaba’ila, faja’alani min khairi kabilihim, summa takhayyaral buyuta, faja’alani min khairi buyutihim, wa’ana khairihim nafsan wa khairuhum baitan – Lallai Allah Ubanagiji Ya halicci halitta sai ya sanya ni mafificinsu, a cikin mafificin tsaransu, sannan ya zabi kabilu, sai ya sanya ni cikin fiyayyar kabila, Sannan Allah Ya zabi Gida, sai ya sanya ni mafi girman gidansu, ni ne mafi girman ‘yan Adam a kan kaina kuma ni ne mafi girmansu gida. “
An karbo daga Wasila dan Asda’i ya ce, Annabi (SAW) Ya ce “ innallahasdafa min waladi Ibrahim Isma’ila, wasdafa min waladi Isma’ila Bani Kinana, wasdafa min Bani Kinanata Kuraishan, wasdafa min Kuraishan Bani Hashim, wasdafani min Bani Hashim – Allah Ya zabi Annabi Ismail daga cikin ‘ya’yan Annabi Ibrahim (AS), Allah Ya zabi Bani Kinana daga cikin ‘ya’yan Annabi Isma’il, Allah ya zabi Kuraishawa daga cikin Bani Kinana, Allah ya zabi Bani Hashimu daga cikin Kuraishawa, sai Allah Ya zabe ni daga cikin Bani Hashim.”
An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce “Allah Ubangiji madaukaki, ya yi zabe a cikin halittunsa, sai ya zabi ‘ya’yan Adam, a cikin ‘yan Adam sai ya zabi Larabawa, a cikin Larabawa, sai ya zabi Kuraishawa, a cikin Kuraishawa sai Ya zabi Bani Hashimu, a cikin Bani Hashim sai ya zabe ni, ban gushe ba ina abin zabi daga cikin zababbu. Kowa ya sani! duk wanda ya so Larabawa, don yana so na ne yaso su, duk wanda ya ki Larabawa, don yana ki na ne ya ki su.
An karba daga Abdullahi dan Abbas yana cewa ”Ruhin Annabi ta kasance haske ce tana gaban Allah tun kafin ya halicci Annabi Adam da Shekaru 2000 (na kirgen Ubangiji), wannan hasken bai gushe ba yana Tasbihi, Mala’iku ma suna Tasbihi da Tasbihinsa, yayin da Allah Ya Halicci Annabi Adam, sai Allah ya sanya wannan Hasken a tsatson Adamu, sai Allah ya saukar da ni kasa a tsatson Adamu (AS), ya sanya ni a tsatson Annabi Nuhu (AS), ya jefa ni a tsatson Annabi Ibrahim (AS), sannan Allah bai gusheba yana ciro ni daga tsatson masu girma (Maza) da mahaifa (Mata) har ya fitar da ni daga Uwata da Ubana, babu wani ko wata da na biyo ta tsatsonta da suka taba zubar da ruwan banza (lalata ko kuma a ce ain masha’a).
‘Yan uwa masu karatu, hakika girman Annabi (SAW) a wurin Allah ba zai misaltu ba, kamar dai yadda muka rika kawowa cikin darussan da muka gabatar a wannan shafi.
Idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu ci gaba da wani darasin in sha Allahu.