Sakamakon mawuyacin halin da ambaliyar ruwa ta jefa daruruwan al’umma a sassa daban-daban a jihar, gwamnatin Jihar Yobe ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA) tare da hadin gwiwar NEMA, sun raba kayan tallafi ga magidanta 457 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kauyuka 17 da ke karamar hukumar Jakusko a Jihar Yobe.
Hukumar SEMA ta gudanar da raba tallafa wa wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa da kayan abinci, kwanon rufi, buhunan siminti, katifu da makamantan su a kauyukan Girgir, Katamma, Amshi, Guyik, Muguram, Jaba, Jakusko, Dumbari, Gwayo, Dukorel, Lafiya, Bayam, Buduwa, Saminaka, Garin Saje, Dachiya da Zabudum, duk a karamar hukumar Jakusko.
- Xi Ya Halarcin Majalisar Shugabannin Kasashen SCO Karo Na 22 Tare Da Gabatar Da Muhimmin Jawabi
- Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Zarce Yadda Ake Tsammani
A zantawarsa da wakilinmu a jihar, Shugaban Hukumar SEMA, Dr Muhammed Goje ya bayyana cewa sun fara samun koke-koken al’ummar wadannan garuruwa dangane da ambaliyar ruwa tun a watan Yuli zuwa Agusta, wanda ta hadin gwiwa da karamar hukumar Jakusko sun gudanar da tantancewa tare da bayyana wadanda abin ya shafa.
Ya ce, “A yau 16 ga watan Satumban 2022, mun raba kayan tallafi ta hadin gwiwar NEMA wanda gwamnatin tarayya ta bayar da nata gudumawa ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa, wanda adadin su ya haura magidanta 400.”
Bugu da kari kuma, a daidai wannan lokaci inda muke raba kayan tallafin, sai kuma ga karin wata ambaliyar ruwa ta abka a wadannan garuruwa, wanda suma yanzu haka suna cikin mawuyacin halin bukatar tallafi.
Saboda haka, tawagar ma’aikatan SEMA za su ci gaba da aiki da karamar hukumar Jakusko domin shiga kowane sako wajen tantance kima da adadin mutanen da wannan ambaliyar ruwan ta shafa, domin ci gaba da tallafa musu kamar yadda Gwamna Mai Mala Buni ya umurce mu.
Ya ce, “Haka kuma, bisa ga halin da ambaliyar ruwan ta jefa jama’a ciki, muna raba wadannan kayan ginin, katifu tare da kayan abinci kai tsaye zuwa ga magidantan da abin ya shafa. Sannan kuma tawagar SEMA da ta karamar hukumar Jakusko za su ci gaba da daukar matakan gaggawa wajen kai dauki ga wadanda abin ya shafa cikin hanzari, kuma a tantance su tare da raba tallafin kai tsaye ga jama’a.”
Karamar hukumar Jakusko da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba wa kokarin gwamnatin jihar Yobe bisa daukin gaggawa da ta kawo wa jama’a a kan lokaci tare da yin kira ga wadanda abin ya shafa da su yi amfani da tallafin cikin adalci domin lamarin ba biyansu asarar da suka yi ba ne, face tallafi ne.