Jumma’ar nan ne, agogon kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron majalisar shugabanin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai karo na 22 a cibiyar taron kasa da kasa ta Samarkand, tare da gabatar da wani muhimmin jawabi.
A yayin jawabin nasa, shugaba Xi ya takaita kwarewar ci gaban da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ta samu, da suka hada da: riko da amince da juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwar moriyar juna, da nuna daidaito, da yin komai ba tare da rufa-rufa ba, da damawa da kowa, da yin gaskiya da adalci.
Ya kuma yi kira ga kasashe mambobin kungiyar, da su kara nuna goyon baya ga juna, da fadada hadin gwiwa a fannin tsaro, da zurfafa hadin gwiwa a zahiri, da karfafa mu’amala tsakanin al’ummomi da musayar al’adu, da tabbatar da hadin kai tsakanin sassa daban-daban. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp