Kimanin mutum 10 ne suka bata a wani jirgin kwale-kwalen da ya kife da yan kasuwar garin Jumbam na karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.
Lamarin ya faru lokacin da suke kokarin tsallaka gadar da ambaliyar ruwa ya rutsa da ita a kauyen Kaliyari, kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Babangida a safiyar yau Asabar.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Yobe Ta Tallafa Wa Magidanta 457 A Karamar Hukumar Jakusko
- Yadda Rugujewar Gadar Katarko Ta Katse Yobe Da Jihohin Borno Da Gombe
Wakilinmu a jihar Yobe ya tattauna da wani ganau jim-kadan da faruwar hatsarin kwale-kwalen, Mallam Ja’afar Nuhu, wanda shi ma daya ne daga cikin ‘yan kasuwar Babangida mai ci mako-mako.
Nuhu, ya bayyana cewa jirgin ya dauko mutum 22, wanda bayan kifewarsa kimanin mutum 10 sun bata, kana mutum 12 sun tsallake rijiya da baya.
“Baya ga kifewar kwale-kwalen kuma an samu gawar wani mutum daya wanda ya yi kokarin tsallaka ruwan.”
Ya kara da cewa, “Hatsarin ya afku da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Asabar, jim-kadan da faruwar hatsarin muka zo nan, a nan inda gadar Kaliyari ta karye. Kuma muma cikin taimakon Allah, jirginmu ya tsallakar da mu lafiya.” Cewar Mallam Ja’afar.