Akalla mutane biyu ne aka tabbatar sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a wani sansani da ake ajiye Tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram da suka mika wuya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Jami’an gwamnatin jihar Borno sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.
Sansanin Koshere na daya daga cikin wuraren da aka ware kwanan nan domin ajiye ’yan ta’addan da suka mika wuya sakamakon bukatar rage cunkoso a sansanin Hajji da aka ware tun farko domin tsugunar da tubabbun ‘yan ta’addan.
Majiyoyi a cikin sansanin sun ce adadin wadanda suka mutu a ranakun Juma’a da Asabar ya zarce 20. Amma jami’ai na sansanin sun yi fatali da adadin, inda suka ce, akwai kuskure a kirgen.
Zuwaira Gambo, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, wadda ma’aikatarta ce ke kula da duk wasu kayayyakin gyara a sansanin, ta tabbatar da cewa, an samu asarar rayuka biyu sakamakon barkewar cutar kwalara da ta shafi da yawa daga cikin fursunonin sansanin na Koshere.