An yi wata arangama tsakanin kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da tsagen kungiyar karkashin ISWAP, a arewa maso gabashin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mai suna Kundu.
BBC ta rawaito Jaridar Daily Trust a Nijeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno.
- Da Dumi-dumi: Mayakan ISWAP Sun Kai Wa ‘Yan Boko Haram Farmaki
- Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno
Wata majiyar tsaro ta ce Kwamanda Kundu tare da tawagarsa na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan babura shida, kowanne dauke da mutum uku suka far musu.
Talla
A baya-bayan nan dai ana yawan samun arangama da juna tsakanin kungiyoyin da a baya suka addabi al’umar kasar.
Talla