Gwamnatin Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ta hana sanya karamin siket a matsayin kayan makaranta a dukkan makarantun jihar.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar, Ngozi Chuma-Udeh, ta bayyana hakan a garin Awka a ranar Lahadi, inda ta ce sanarwar dakatarwar ya zama wajibi ganin cewa, makarantun za su koma azuzuwa a ranar Litinin.
Ta ce an sanar da dakatarwar ga sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Kwamishiniyar ta yi Allah-wadai da yadda ake samun karuwar sanya kananan siket a matsayin kayan makaranta Wanda hakan ba daidai ba ne kuma ba za a amince da shi ba ga yara masu zuwa makaranta.
Kwamishiniyar ta ce an bukaci dukkan ma’aikatan da lamarin ya shafa su tabbatar da cewa makarantun sun bi umarnin don ceto makomar daliban jihar.