Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke sintiri a kan babbar hanyar Okene zuwa Abuja, a ranar Asabar, 17 ga watan Satumba, 2022, sun kama wata motar bas J-5 dauke da bindigogi guda 18 da harsashi 1,300 a jihar Kogi.
Motar ta fito ne daga Onitsha, jihar Anambra ta nufi hanyar Kaduna-zaria a jihar Kaduna.
NDLEA ta ce an kama mutane biyu da ake zargi da rakiyar makaman, Chukwudi Aronu mai shekaru 51 da Shuaibu Gambo mai shekaru 23.
Rahoton ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a ranar Lahadi.
Ya ce, “Hukumar ta kuma cafke wani Anthony Agada mai shekaru 37, dauke da harsashi 1,000 a cikin wata motar bas da ta taho daga Onitsha zuwa Abuja duk a rana daya (Lahadi).”
A wani samame da jami’an NDLEA suka yi, an kama kwalaben codeine 1,404 da kuma ampoules na allurar pentazocine guda 2,040 a wata mota da ta taho daga Onitsha zuwa Sokoto, wacce aka rubuta ‘mai karba: Stanley Raymond mai shekaru 39, mai aikawa: Shadrack Ifedora mai shekaru 46.