Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Kara himma kan aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla dake jihar Taraba.
Sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen taronsu na bakwai da suka gudanar a karshen mako a gidan gwamnatin Gombe dake jihar.
An rahoto cewa gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun yi taron ne a Gombe domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin da kuma kasa baki daya.
A cikin sanarwar da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karanta a karshen taron, Gwamnonin sun nuna damuwarsu kan halin da ake ciki na wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas.
Buni ya ce Jihohin shida na karbar kasa da kashi biyar cikin dari na kasafin wutar lantarki na kasa yayin da su ke da kashi 14 cikin 100 na al’ummar kasar da kuma kashi 30 na fadin kasar Nijeriya.