Jami’an Hukumar yaki da sha da safafar miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wasu Kwalaben kayan maye guda 26,600 da take zargin wani mai suna Qasim Ademola ya yi safararsu a Kano.Â
Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce, kayan mayen ciki har da na Akuskura.
Femi a cikin sanarwar da ya fitar a garin ya ce, hukumar ta kama Qasim ne, a ranar 13 ga watan Satumbar 2022 a yayin da yake kokarin tura kayan zuwa wasu sassan kasar nan.
Ya ce, jami’an hukumar sun kwace kayan a ranar 15 ga watan Satumbar 2022 a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano daura da Gadar Tamburawa.
Femi ya ce, Qasim dan shekara 39 ya fito ne daga karamar hukumar Akinyele a jihar Oyo, inda kuma jami’an hukumar, suka kamo sauran mutane uku biyo bayan bin Sahu da jami’an suka yi.