Gwamnatin Jihar Kano ta nuna rashin jin dadinta game da yadda ake zubar da sharar a unguwar Kabara da ke bayan fadar Sarkin Kano a cikin birnin jihar.
Kwamishinan Muhalli na Jihar, Dakta Kabiru Getso ne ya bayyana hakan bayan sa ido kan yadda ake tsaftace muhalli a Kano a duk wata a ranar Asabar.
- 2023: Mace 1 Ce Ta Fito Takarar Shugaban Kasa Da Wasu 380 A Kujerun Majalisar Tarayya – INEC
- Ba Mu Tauye Wa Kowa Damar Mallakar Katin Zabe A Kasar Nan Ba – INEC
Ya ce zubar da shara a wuraren da ba a kebe ba alama ce ta rashin dabi’a ta mutane game da tsabtace muhalli da lafiya.
A cewar Getso, “Mutanen da ke zubar da shara a kan hanyoyinmu makiyan jihar ne kawai kuma muna gargadinsu. Ba su da wani alheri ga mutanen Kano.”
Getso ya jaddada cewa zubar da shara a kan titunan birni na iya haifar da yaduwar cututtuka da sauran haduran muhalli.
Kwamishinan, ya yaba wa Kungiyar Danagundi Mutaimaki Juna Development Association (DAMJUDA), kungiyar taimakon kai da kai, bisa kokarinta ta hanyar share yankinsu.
Ya yi kira ga sauran al’umma da kungiyoyin taimakon kai da su yi koyi da su.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa a yayin rangadin, kotunan tafi da gidanka da ke da alaka da kwamitin kula da tsaftar mahalli ta jihar sun kama wasu mutane 80 da suka saba wa doka.
Sun biya tarar Naira 70,400 gaba dayansu.