Miliyoyin manoma a kasar Sin, sun gudanar da bikin girbin amfanin gona na bana a Juma’ar nan, bikin irin sa na 5 da aka kirkira domin murnar samun yabanya mai yalwa.
A bana ma an gudanar da bikin a sassan kasar Sin daban daban, yayin da ake hasashen samun amfanin gona mai yawan gaske, duk da bazuwar annobar COVID-19, da tsananin zafi da aka fuskanta a shekarar.
Bayan haye kalubalen ambaliyar ruwa da aka samu gabanin shiga hunturu a shekarar bara a yankin arewacin kasar, da lattin shuka alkamar hunturu, da sake bazuwar annobar COVID-19, da tsanantar yanayin zafi da fari a wasu sassan kudancin kasar, an samu karuwar hatsi da aka noma a yayin bazara, da shinkafa ‘yar wuri a wannan kaka ta bana.
An fara gudanar da bikin girbin amfanin gona na kasar Sin ne a shekarar 2018, yana gudana kuma a daidai lokacin da tsayin sa’o’in rana ke yin daidai da na dare, daya daga cikin lokuta mafiya muhimmanci 24, a kalandar noma ta gargajiyar Sin, ya kan kuma fado ne duk shekarar tsakanin ranekun 22 da 24 ga watan Satumba, a lokacin da ake tsaka da girbin amfanin gona. (Saminu Alhassan)