A yau Talata Jami’an Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun hallara Dandalin Eagle Square da ke Abuja domin sa ido kan yadda za a gudanar da zaben fidda gwani na jamiyyar APC mai mulki.
Rahotanni sunce, bayan Jami’an sun zagaya wajen da za a gudanar da zaben sun kuma tsara kansu wuraren tsaya wa a Dandalin na Eagle Square.
Sai dai Jami’an ba su ce uffan kan dalilinsu na zuwa Dandalin ba.
Zuwan na Jami’an Dandalin ana ganin ya biyo bayan rahotannin da akai ta wallafa wa na cewa ‘yan takarar shugaban kasa sun yi Ta sayen Wakilai da za su jefa kuri’a da kudade da yawa.