Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, adadin kudin shigar da aka samu daga sayar da kayayyakin manhajar masana’antun kasar Sin a watanni bakwai na farkon bana, ya kai kudin Sin yuan biliyan 121.9, adadin da ya karu da kaso 8.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Ci gaban manhajar masana’antu, yana taka babbar rawa wajen zamanintar da masana’antu. A cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, gwamnatin kasar Sin ta fitar da manufofi, domin nuna goyon baya ga ci gaban manhajar masana’antu, tare kuma da hanzarta saurin kafa manyan kamfanonin kera kayayyakin manhajar masana’antun.
Alkaluma sun nuna cewa, kasuwar manhajar masana’antun kasar Sin tana kara habaka sannu a hankali a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, karfin samar da kayayyakin shi ma ya karu, haka kuma yanayin raya sana’ar ya inganta, duk wadannan suna taimakawa ci gaban sana’ar kera kayayyaki na zamani, kawo yanzu gaba daya adadin kamfanonin da suka shafi manhajar masana’antu a fadin kasar Sin, ya kai sama da dubu 542. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)