Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kai wani samame a maboyar ‘yan bindiga, a cigaba da gudanar da aikin share maboyar ‘yan bindigan da suka addabi yankin Kuriga-Manini-Udawa, da ke kan iyakar Chikun-Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan acikin wata sanarwa da yafitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, sojojin sun gudanar da aikin lalubo maboyar da ke kusa da Ungwan Malam Ali.
Aruwan ya ce sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda tasa dole ‘yan ta’addan suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Sanarwar ta cigaba da cewa, sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya, alburusai 18, da kuma bindiga kirar gida guda 11.
“Sojojin sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su, wadanda aka bayyana sunayensu kamar haka: Luka Ibrahim, Yusuf Jibril da Saminu Abdullahi.”
Aruwan ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna tana yabawa sojojin bisa nasarar share maboyar ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.