Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja ta hannun babban sakataren ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore.
Ministan ya taya ‘yan Nijeriya murnar samun ‘yancin kai tare da tabbatar wa ‘yan kasar kudurin gwamnati na tinkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.
Ministan ya umurci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan damar wajen yin tunani kan kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta da kuma rawar da za su iya takawa wajen magance su.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi aiki tukuru tare da guje wa duk wani aikin laifi don samun arziki ta hanyar da bata dace ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp