Yayin da ake bukukuwan cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Argentina, a jiya Laraba, an gudanar da babban dandalin musayar al’adu tsakanin sassan biyu a nan birnin Beijing, inda a yayin zaman, manyan jami’ai daga kasashen biyu suka sha alwashin ci gaba da ingiza manufar nan ta samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.
Sama da wakilai 100 daga tsagin Sin da na kasar Argentina ne suka halarci dandalin, wanda kafar CMG da gungun kafofin yada labarai na Argentina suka dauki nauyin shiryawa.
Kaza lika dandalin ya kasance daya daga ayyuka daban daban, na yaukaka kawancen kasashen biyu da aka shirya gudanarwa a shekarar nan ta 2022. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)