A baya-bayan nan, shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama ne, suka bugu waya ko aiko da wasiku ga Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban jamhuriyar jama’ar kasar Sin, don taya murnar cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, tare da fatan samun nasarar gudanar da babban taron wakilan JKS karo 20 dake tafe.
A sakonsa, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi fatan babban taron wakilan JKS karo na 20, wanda ke da ma’ana a tarihi, zai gudana cikin nasara.
Ya kuma bayyana cewa, yana fatan taron zai fito da wani tsari na ci gaban kasar Sin a nan gaba. Ya kara da cewa, Najeriya na son karfafa cudanya da hadin gwiwa da kasar Sin, da ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Shi ma shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai da’awar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, da cudanyar bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaito a duniya.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuduri aniyar tallafawa ci gaban kasashen Afitrka baki daya.
Shugaba Akufo-Addo, ya bayyana cewa, kasarsa na fatan sassan biyu, za su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu da hadin gwiwar bangarori daban-daban, da karfafa dankon zumunci a tsakanin al’ummominsu, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.
A madadin gwamnatin da jama’ar kasar Afirka ta Kudu kuwa shugaban kasar Cyril Ramaphosa, ya mika gaisuwa da taya murna ga shugaba Xi da gwamnati da jama’ar kasar Sin, yana mai jaddada cewa, kasarsa a shirye take ta kara karfafa zumunci da abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin ta da kasar Sin. (Ibrahim Yaya)