Wata kotu dake birnin tarayya Abuja ta tabbatar da zaben Hon. Christopher Maikalangu Dan Jam’iyyar PDP a matsayin shugaban karamar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC).
A hukuncin da aka yanke, kotun mai alkakai Uku da ta hada da Hon. Mai shari’a S. B Belgore (Shugaba), Hon. Justice Yusuf Halilu (mataimaki na 1), Hon. Mai shari’a Jude O. Onwuegbuzie (mataimaki na 2) ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben karamar hukumar FCT ta yanke a ranar 5 ga watan Agusta, wadda ta bayyana Hon. Murtala Usman Karshi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 12 ga watan Fabrairu.
Alkalan sun ce hukuncin da kotun karamar Hukumar ta yanke, ba ma shirme ne kadai ba, kotun ta yi watsi da duk nasarorin da aka samu a dimokuradiyyar Nijeriya.
Yayin da yake karanto hukuncin da aka yanke a karar FCT/ACEAT/AP/01/22, wacce ta samu Maikalangu na jam’iyyar PDP a matsayin mai shigar da kara da Murtala Karshi da wasu uku a matsayin wadanda ake kara, Hon. Mai shari’a Yusuf Halilu, ya ce karamar kotun ta yi kuskure ne ta hanyar yin watsi da hujjoji da aka baje mata a gabanta.
Alkalan sun ce, karamar kotun ta yi kuskure ta hanyar ayyana Karshi a matsayin wanda ya lashe zaben.