Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya umurci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar jihar Sakkwato da ta koma karatu ko kuma ya dakatar da basu albashi.
Gwamnan a wajen bikin cikar Nijeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai da aka gudanar a jihar, ya kalubalanci reshen kungiyar kan yadda mambobin kungiyar ke karbar albashinsu duk da cewa sun marawa takwarorinsu na tarayya ba.
Ya bukace su da su sake duba matsayar su, su koma bakin aiki, inda ya ce batutuwan da rassan ASUU a jami’o’in tarayya suke bukata, ba daya suke ba da abin da jami’ar jihar ke bukata.
Gwamnan ya ce, idan Malaman Jami’ar suna da wasu abubuwa da suke bukata, to su fito da su, in ba haka ba, ba zai sake biyansu albashi ba har sai sun koma aji.