Manya da kananan ofisoshin jakadancin kasar Sin dake sassan daban-daban na duniya, sun gudanar da bikin murnar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar jama’ar kasar Sin, yayin da wasu kungiyoyin kasa da kasa suka bayyana fatansu na alheri ga babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 dake tafe da kara fatan yin hadin gwiwa.
Babbar darektar ofishin MDD dake Geneva Tatiana Valovaya, da babban darektan hukumar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya Daren Tang, da babban darektan kungiyar kwadago ta kasa da kasa Guy Ryder, da babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya Ngozi Okonjo-Iweala, da sauran shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da wakilan din-din-din na kasashe daban-daban dake Geneva, duk sun bayyana jin dadinsu tare da yaba irin dimbin nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin shekaru 10 da suka gabata, inda suka yi fatan za a gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 20 cikin nasara.
Sun kuma bayyana fatan ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban, tare da fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya da bunkasuwar duniya.(Ibrahim)