Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a 7 ga watan Oktoba, 202 zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na N19.76tn a zauren majalisar dokokin Nijeriya.
Za a gabatar da kasafin ne da misalin karfe 10:00 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin gadi da ke cikin harabar majalisar ta kasa.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ne ya bayyana hakan a safiyar ranar Talata a lokacin da yake karanta wasikar shugaba Buhari ga ‘yan majalisar kan shirinsa na gabatar da kasafin kudin shekarar 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp