Kotun da ke sauraren karar kisan da wani dan China, Mista Geng ya yi budurwarsa Ummita a Jihar Kano, ta dage zamanta.
An dage zaman kotun har zuwa ranar 27 ga watan Oktoba har sai an samarwa da Mista Geng Quangrong, wanda zai yi masa tafinta daga Yuranci zuwa Chanisanci.
- Yadda Wasu Mata 2 Suka Haifi Jarirai Shida-Shida A Yobe
- ‘Yan Sintiri Sun Kashe ‘Yan Bindiga 12 A Jihar Taraba
Ba a jima da fara zaman kotun ba ne aka dage zaman saboda matsalar rashin fahimtar bayanai daga bangaren Mista Geng, wanda ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari, da aka fi sani da Ummita, a Kano.
A zaman da kotun ta yi a baya, Mista Geng ya nemi a ba shi damar daukar lauyan da zai kare shi.