Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya kara ta’azzara inda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka maka shugabanni jam’iyyar a gaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) bisa zargin almubazzaranci da kudade, sata da mika jabun takardu da dai sauransu.
‘Yan jam’iyyar masu neman madafun a zaben 2023 ne, suka aike da kokensu ga shugaban hukumar EFCC kan lamarin.
Ko’odinetan jam’iyyar, Chris Ogbu ne ya sanya wa karar hannu a takardar koken mai kwanan wata ranar 30 ga Satumba, 2022; da Sakatare, Dauda Yusuf, da Sakataren Yada Labarai, C. Ikenta.
Musamman masu shigar da karar, sun bukaci hukumar da ta binciki shugabannin jam’iyyar tare da gurfanar da su gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudaden jam’iyyar da karkatar da kudade ba bisa ka’ida ba, cin hanci da kuma amfani da takardun bogi.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Sanata Iyorchia Ayu (Shugaban jam’iyyar), Sanata Samuel Anyanwu (Sakataren jam’iyyar na kasa) da Umar Iliya Damagnum (Mataimakin Shugaban jam’iyyar (Arewa).