Jiya Talata 4 ga wata, an yi babbar muharawa dangane da batutuwan wariyar launin fata, da nuna kiyayya ga baki, da rashin hakuri, a yayin taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 51.
A yayin muhawarar, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland Jakada Chen Xu, ya yi jawabi a madadin kasashen da ke da ra’ayi kusan iri daya da na kasar Sin, inda ya nuna matukar damuwa kan yadda ake nuna bambanci, ga ‘yan kananan kabilu, yayin da ake aiwatar da doka a wasu kasashe, ya kuma bukaci kasashe masu ruwa da tsaki da su kalli kansu yadda ya kamata, a fannin mummunar matsalar wariyar launin fata, su yi cikakken bincike, da kyautata hukumominsu, da dokokinsu, da manufofinsu, da matakansu masu nasaba da wariyar launin fata, a kokarin aiwatar da “sanarwa da tsarin ayyuka na Durban” yadda ya kamata.
A cikin jawabinsa, Chen Xu ya yi nuni da cewa, yadda hukumomin aiwatar da doka suke nuna bambancin launin fata, da yin amfani da karfin tuwo yayin da suke aiki, sakamako ne da wadannan kasashe suka samu, saboda sun dade suna fama da matsalar wariyar launin fata, da rashin daidaito cikin zamantakewar al’umma bisa tsari, kana matsala ce da ya zuwa yanzu ba su warware ta ba, tun bayan cinikin bayi da mulkin mallaka.
A cikin wadannan kasashe, an dade ana nuna wa ‘yan asalin Afirka, da Asiya, da musulmai, da sauran ‘yan kananan kabilu bambanci, da daukar su mutane marasa muhimmanci, ana kuma keta dokokinsu, kuma ko da yaushe suna fuskantar barazanar cin zarafi.
Cikin jawabinsa, Chen Xu ya yi kira ga kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, da ofishin babbar jami’ar kula da hakkin dan Adam na MDD, da su kara mai da hankali kan batutuwa masu nasaba da wariyar launin fata, da tashin hankali da aka ambato, tare da daukar matakan da suka wajaba na magance hakan. (Tasallah Yuan)