Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da sunaye 837 na ‘yan takarar gwamna da na mataimakan su, waɗanda za su fafata a zaɓen 2023.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC Festus Okoye ne ya bayyana sanarwar fitar da sunayen a shafin yanar gizo na INEC, a ranar Laraba.
Sunayen dai su na da yawan da ya kai shafuka 894, waɗanda su ka haɗa na ‘yan takarar gwamnoni da mataimakan su 837, sai kuma na masu takarar majalisar dokoki har mutum 10,231.
Okoye ya ce za a yi zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin a jihohi 28.
Ya ƙara da cewa tun a ranar 12 ga Agusta, 2022 INEC da kulle damar canja ɗan takara ko janyewa, sai fa idan lamari ne na mutuwa ya ratsa.
“Kai ko da ɗan takara ne ya mutu, to tilas sai dai kotu ce za ta bai wa INEC iznin amincewa ta amshi sunan wanda zai maye gurbin sa, kamar yadda Dokar Zaɓe ta Sashe na 34 (1) ta 2022 ta gindiya.”
Okoye ya ce jam’iyyu 18 ne su za su yi takarar zaɓen gwamna da na Majalisar Dokoki.
Cikin makon shekaranjiya ne wannan jarida ta buga labarin cewa za a fafata da mata 380 cikin ‘yan takarar kujerun Majalisar Dattawa da ta Tarayya su 4,224.
A jadawalin sunayen ‘yan takarar da ta fitar, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an samu mace ɗaya tilo ta fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Hakan na ƙunshe cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar, mai ɗauke sa hannun Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye.
Ya ce an samu mata har 380 da za a fafata neman kujerun Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa da su.
A jerin sunayen an lissafa mata 92 masu neman kujerar Majalisar Dattawa, sai kuma wasu mata 288 da za a fafata neman kujerar Majalisar Tarayya da su.
A ɓangaren maza kuwa, INEC ta buga sunayen 1,008 masu neman kujerar Majalisar Dattawa, sai kuma wasu 2,832 da za su fafata neman kujerun Majalisar Tarayya.
INEC ta ce jam’iyyu 18 ne su ka shiga takarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a fafata a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
“An samu masu takarar shugaban ƙasa da masu takarar mataimakin shugaban ƙasa har su 35 daga jam’iyyu 18. Akwai ‘yan takarar Majalisar Dattawa su 1,101, waɗanda a cikin su 92 mata ne. Sai kuma masu takarar Majalisar Tarayya su 3122.
“Za a yi takarar kujeru 109 a Majalisar Dattawa, sai kuma kujeru 360 a Majalisar Tarayya. Baki ɗaya kujeru 469 kenan.” Inji Okoye, wanda ya ƙara da cewa waɗannan ‘yan takara na majalisu sun zama 4,224 kenan.
Cikin waɗanda INEC ta wanke domin shiga takarar zaɓen Shugaban Ƙasa, har da Bola Tinubu na APC, Rabiu Kwankwaso na NNPP, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.
Sai dai kuma duk da jam’iyyar ADC ta dakatar da Kachikwu ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, sunan sa ya fito a cikin waɗanda za su fafata.
A jerin sunayen masu takarar Majalisar Dattawa dai babu sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan na APC da Machina wanda su ke tankiyar cancantar shiga takarar a tsakanin su.