Tsohon shugaban riko na karamar hukumar Toro da ke Jihar Bauch, Alhaji Shehu Buba ya bukaci al’ummar Fulani Makiyaya a fadin kasar nan da su manta da duk bambancin da ke tsakaninsu kafin su iya tunkarar matsalolin da ke gabansu na shafa musu kashin kaji kan matsalar tsaro.
Tsohon shugaban riko na karamar hukumar Toro ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi ga dubban Fulani makiyaya da suka halarci bikin kaddamar da asusun neman taikon ilimin ‘ya’yan Fulani makiya, wanda kwamitin Jange-Dure karkashin Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunaht (JIBWIS) ta gudanar a garin Magama Gumau da ke Jihar Bauchi.
- Ranar Abokan Hulɗa: NIS Ta Karrama Jami’anta Masu Aiki Tuƙuru
- Kotu Ta Yanke Wa Wani Tsoho Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Har Abada Kan Laifin Fyade A Jigawa
Ya ce Fulani za su sami kubuta daga irin halin da suka sami kansu na musgunawa a cikin kasar su ta haihuwa ne kawai in har suka hada kansu suka zama sinsiya madaurinki daya wajen tafiyar da harkokin rayuwarsu.
Alhaji Buba wanda ya mika wa kungiyar motar bas sabuwa na jimillar naira miliyan biu darabi, ya yaba wa kwamitin Jange-Dure bisa namijin kokarin da ta yi wajen sauya rayuwar ‘ya’yan Fulani da ke a kowane sako da lungu na kasar nan.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Shiekh MuhammaduSani Yahaya Jingir, ya bukaci Fulani Makiyaya da ke cikin kasar nan da su kara hada kansu wajen tafiyar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum don magance matsalar da wadansu miyagun mutane ke yi na shafa masu bakin fenti.