Wasu kungiyoyin mata sun shirya wani taro na musamman ga mata zalla kan muhimmancin koyi da halayen fiyayyen halitta, Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW), musamman a bangaren tausayinsa da kyautatawarsa.
Zaman wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, an yi shine don murnar zagayowar watan da aka haifi Annabi Muhammad SAW, na bikin Maulidin bana.
Wannan shi ne karon farko da mata suka fito suka shirya irin wannan taro ga junansu, wanda ta mai da hankali ga baje-kolin halayen manzon Allah Annabi Muhammad SAW, domin a kara fahimtar su tare da yin koyi da su.
Dakta Habiba Yahaya Alfadarai, wato daya daga cikin wadanda suka shirya taron ta ce Annabi ya yi wa mata cikakken gata, kuma babu abin koyi fiye da shi.
Irin wadannan kyawawan halaye na manzon Allah, SAW, idan aka yi koyi da su, sun isa magance dimbin matsalolin da ake fama da su a kasar, kamar yadda Sayyada Rahama Abdulmajid, wadda ita ma ta gabatar da lacca ta faÉ—a.
Wadanda suka gabatar da lacca a wajen taron dai sun bayyana cewa yana da kyau a ci gaba da nuna soyayya ga Annabi Muhammad SAW, amma kuma zai fi kyau a nuna soyayyar a aikace ta hanyar aiki da koyarwarsa. BBC Hausa