Harajin da aka nemi kakabawa kasar Sin ba su kai ga nasara ba a fannin tattalin arziki da siyasa da ma fannin doka. A kwanakin baya ne, jaridar Capitol Hill ta Amurka ta wallafa wani sharhi dake tabbatar da cewa, yakin cinikayya tsakanin Amurka da Sin, bai kai ga nasara ba.
A zahiri ma, wannan ba sakamako ne mai kyau ba tun daga farko. Yakin kakaba haraji da Amurka ta ayyana kan kasar Sin sama da shekaru 4, ya nuna cewa, cin mutunci a alakar kasa da kasa ba zai taba zuwa ko’ina ba. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)