Mai magana da yawun babban taron wakilan JKS Sun Yeli, ya bayyana cewa, gobe Lahadi 16 ga wata ne, za a bude babban taron wakilan JKS karo na 20 da misalin karfe 10 na safe, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, za kuma a kammala taron a ranar 22 ga watan Oktoba, inda za a shafe kwanaki 7ana gudanar da shi.
Bugu da kari Sun ya bayyana cewa, an tabbatar da cancantar wakilai dubu 2 da 296 wadanda za su halarci babban taron wakilan JKS karo na 20. inda za su wakilci mambobin JKS sama da miliyan 96 da kuma sama da miliyan 4.9 a matakin farko na kungiyoyin jam’iyyu.
An tattara ra’ayoyin jama’a sama da 4,700 game da daftarin rahoton kwamitin koli na JKS na 19 da aka gabatarwa babban taron wakilan JKS karo na 20.
Wakilan sabon zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS karo na 20, za su gana da manema labarai na kasar Sin da na kasashen ketare bayan kammala cikakken zama na farko na kwamitin kolin JKS na 20. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)