Wasu mutane goma sha daya (11) sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas kuma suka gamu da munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya wakana a daidai kauyen Jaki da ke kan hanyar Alkaleri zuwa Gombe a cikin karamar hukumar Alkaleri da ke cikin jihar Bauchi a ranar Asabar.
Tara daga cikinsu sun mutu ne nan take a yayin da sauran biyun kuma suka mutu bayan da aka kaisu babban asibitin Alkaleri da kokarin ceto rayuwarsu inda likita ya tabbatar da cewa su dim ma sun mutu, adadin da ya jawo mutum 11 da suka rigamu gidan gaskiya sakamakon hatsarin.
Kwamandan shiyya na hukumar kiyaye auku hadura ta kasa (FRSC) a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, shi ne ya tabbatar da hakan ga ‘yan jarida a ranar Lahadi, ya kara da cewa, hadarin ya hada da wata motar kabu-kabu mallakin Yankari Express (Mallakin gwamnatin jihar Bauchi) da kuma wata motar kamfanin Dangote.
Abdullahi ya misalta cewa hatsarin ya faru ne sakamaon tukin ganganci, “Manyan mutane maza ashirin ne suka gamu da hadarin.
“11 sun rigamu gidan gaskiya. Sannan, takwas kuma sun gamu da munanan raunuka, amma suna amsar kulawar kilitoci a babban asibitin Alkaleri,” ya shaida.
Yusuf ya shawarci matuka motoci da a kowani lokaci suke bin ka’idojin tuki da kauce wa yin tukin ganganci domin kula da lafiyarsu da rayukarsu, kana ya nemi su kauce wa tsula gudun tsiya.