A kalla mutane 23 ne ciki har da jami’in hukumar ‘yan sanda aka kashe, yayin da wasu mutum 11 suka gamu da munanan raunuka sakamakon wani harin da wasu ‘yan bindiga dadi suka kaddamar a kauyen Gbeji da ke karamar hukumar Ukum a jihar Benue a ranar Laraba.
Mai bai wa gwamnan Jihar Benue shawara kan harkokin tsaro, Liyutanal Kanal Paul Hembah (Mai murabus) shi ne ya shaida hakan a hirarsa da wakilinmu ta wayar tarho, ya kara da cewa, dan sandan da ya gamu da munanan raunuka ya mutu a lokacin da ake hanyar kaisa asibiti.
Sanann, da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Wale Abass, a hirarsa da ‘yan jarida, ya ce, makiyaya biyar su ma sun mutu tare da dan sandan.
Ya ce, tunin aka tura ‘yansandan da takwarorinsu ba tsaro domin farfado da zaman lafiya a yankin.
Wani mazaunin yankin, Elder Iorngaem Kerepe, ya ce, baya ga wadanda aka kashe, maharan sun kuma kona gidaje sama da 50.
Shi ma da yake magana kan harinz Shugaban karamar hukumar Ukum, Tyoumbur Kaatyo, ya nuna kaduwarsa da wannan harin, yana Mai cewa an kwashi gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki a asibiti tare da daukan wadanda suka jikkata dukka zuwa asibiti a Afia.
Mai bai wa gwamna shawara kan tsaron ya bada sunayen mutanen aka kashe din da Mtem Torpav, Eje Abraham (Dan sanda), Zege, Afam Abama, Akor Jem, John Nor, Torlumun Orabende, Orpandega Terseer, Bem Nyichia, Atseva Ortwer, Mrs. Torsar,Nyave Tyoulugh, Kpaver Tion, Ugba Joseph,
Mbakumbur Peter, Moses Pav,
Apeseza Baba, da kuma Unduun.