• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ICPC Ta Rufe Makarantu 68 Na Bogi A Nijeriya

by Sadiq
3 years ago
ICPC

Hukumar da ke Yaki da Almundahana da Sauran Laifukan Cin Hanci (ICPC), ta ce ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri ta bogi 62 a fadin kasar.

Hukumar ta ce wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Nijeriya, domin kuwa babu wata jiha a fadin kasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta.

  • Dan Shekara Hudu Ya Kubuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Yobe
  • PDP Ta Zargi Makiyan Dimokuradiyya Da Kitsa Hargitsi A Gangamin Da Jam’iyyar Ta Yi A Kaduna

Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye, ta kai ga gano adadin makarantu da suka hada da jami’o’i da kwaleji-kwaleji 62 na bogi da ke bayar da shaidar digiri a fadin Nijeriya.

Amma ta ce an fi samun irin wadannan makarantu a arewa ta tsakiyar Nijeriya.

ICPC ta ce ta bayyana wannan gagagrumar barna ne, domin shaida wa ‘yan Nijeriya cewa tana kallon duk wani mai shirin yin almundahana a kowane fanni.

LABARAI MASU NASABA

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

Ta ce ko da za a dauke kai a ko ina, to ba dai a bangaren ilimi ba, domin kuwa duk kasar da ba ta da tsarin ilimi ingantacce, to gobenta za ta iya kasancewa cikin kila wa kala.

Muhammad Ashiru Baba shi ne shugaban sashen wayar da kan jama’a na ICPC, ya kuma ce abin takaici ne halin da ilimi ya tsinci kansa a Nijeriya.

Ya kara da cewa ”mafi yawan Jami’o’in ba su da ginin kansu, a maimakon haka suna amfani da gine-ginen Sakandire da na Furamaren da ba a karatu a karshen mako domin gudanar da karatunsu, kuma cikin shekara guda mutum zai samu shaidarsa”.

Wanda hakan ke nufin iyayen da suke kai yaransu irin wadannan wurare, sun kwana da sanin inda suke kai yaran nasu ba wajen kwarai ba ne.

Ashiru Baba ya ce a kwanakin baya har kama sansanin ‘yan bautar kasa suka yi na bogi, wani abu da suka jima yana daure musu kai.

ICPC ta cimma nasarar kulle wadannan jami’o’i ne ta hanyar bayanai da ta samu daga hukumar da ke kula da Jami’o’i ta kasa NUC, kuma tun daga 2016 ta ke gudanar da wannan aiki har ya zuwa yau.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno
Manyan Labarai

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya
Manyan Labarai

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?
Manyan Labarai

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Next Post
Zan Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu Da Ya Soke Takarata – Aisha Binani

Zan Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu Da Ya Soke Takarata - Aisha Binani

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno

November 4, 2025
Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha

November 4, 2025
China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.