Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi Al’umma, Rayuwar Matsa (Soyayya), Rayuwar yau da kullum, Zamantakewa, Zaman aure, da dai sauransu. A yau shafin namu zai yi duba ne game da abin da ya shafi rayuwar al’umma, musamman ta fannin abin da ya fi damun al’umma a wannan lokacin.
Wanda a tawa fahimtar hakan ba komai ba ne face Talauci, Jahilci, Rashin tsaro, Cututtuka, Rashin kayan more rayuwa, Rashin kyawawan Tituna, Rashin wutar lantarki da dai sauransu.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu, Ko me yake Janyo afkuwar hakan? Ta wacce hanya za a magance matsalar?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:Zeenatu Ahmad Isyaku daga Jihar Kaduna:
Abin da ya fi damun al’umma a wannan kasa ta mu shi ne; na farko akwai matsalar Yunwa, Talauci, Rashin tsaro da kuma rashin aikin yi. Toh zan iya cewa rashin samun shuwagabanni masu tausayawa al’umma a kasarmu.Ta yadda za a magance wannan matsala shi ne; Samarwa ‘yan kasa abin da suke bukata da kuma samun shuwagabanni masu tausayawa al’umma.
Bilkisu Ridwan daga Funtua Jihar Katsina:
Abin da ya fi damun Al’umma a wannan lokacin shi ne; Talauci. Rashin shugabanci nagari da kuma kowa na shi ya sani taimako ya yii karanci a zukatan al’umma. Hanya mafi sauki shi ne; mu zabi sabon shugaba ba wanda ya shekara talatin yana neman mulki ba.
Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
Ai abin a bayyane yake domin sanin kowa ne Al’ummar Nageriya suna cikin wani, mayucin halin kuwa Yunwa babbar matsala ce, da yawan marasa karfin mutane na fuskantar kalubale na rashin abinci, saboda abinci ya yi wuya ya masifar tsada, daga shinkafa, gero, dawa, masara babu abin da ke tabuwa, a yau man gyada da manja sun haura naira dubu talatin har gishiri nan ya yi tsada bare garin kwaki da sukari, da wanne talaka zai ji? da wanne marasa aiki za su ji? maganar gaskiya wannan abin takaici ne ga ‘yan kasa, ace a cikin kasar su basu da ‘Yanci abin da za su jefa a bakin salati sai su yi sati ba su samu ba, lokaci yana lokaci sai dai addu’a.
Abin a bayyane yake rashin tsoron Allah da almundahana sannan da cin hanci da rashawa da cin amana da rashin adalci shi ne ya janyo hakan. Hanya daya ce shugabannin mu tun daga matakin shugaban kasa har zuwa kansila su ji tsoron Allah, su sani talakawansu na cikin halin wuya, idan su sun ci mai kyau sun sha me dadi to na kasa da su ko marar dadin su na nema, ya kamata ku sani Kwabo bayan kwabo sai kun yi bayanin yadda ku ka same su da yadda ku ka batar da su, bugu da kari hakkokin na nan kan wuyoyinku, muna bukatar ayyukan yi muna bukatar tsaro muna bukatar saukin kayan abinci a karshe mu ma ‘Yan kasa sai mun ci gaba da addu’a Allah ya kawo mana sauki da agaji ya magance mana matsalolin da su ka yika Æ™asar mu kaka gida.
Amina Ahmed Dillara daga Jihar Kaduna:
Talauci, Yunwa da Rashin tsaro, Rashin aikin yi ga matasa da mata, da kuma laifin gwamnati.
Ta hanyar samar da sana’ar hannu ga matasa, su kuma mata a taimaka musu da jari da za su fara sana’ar cikin gida, su kuma gwamnati ya kamata su yi nazari sosai akan yadda za su samar ma da matasa aikin yi saboda a samu sassauci ta bangaren tsaro, saboda idan har matashi yana da inda zai je ya yi aiki, ya samu abin rufin asiri ba ruwansa da bin abokanan banda daga nan ya fara shaye-shaye daga nan kuma sai ya zarce.
Hafsat Yusuf Muhammad Jihar Kano:
Abin da ya fi damun Al’umma a wannan lokacin shi ne; Talauci da Tsadar rayuwa duk abin da za ka yi sai da kudi toh kuma ba a sa munsu kudin dole a shiga wani yanayi sai dai Alllah.
Abin da ya jawo hakan tsadar rayuwa ce, komai ya tashi yadda kake siyan abu to yanzu ba haka yake ba, yau idan ka siya anjima ko gobe sai ka ji an ce ya tashi, wannan rayuwa sai addu’a. Yadda za a magance matsalar nan shuwagabanninmu za su fara magance ta sannan da musu kayan masarufi da kuma addu’a Allah ya sa mu dace ameen.
Yahaya Ibrahim Kaura Jihar Zamfara:
Fargaba da rashin aminci tsakanin Junanmu, ga kuma Talauci. Allah Shi ne; silar faruwar komai da kuma shuwagabanninmu. A koma ga Allah a yawaita Istikfari da kuma yin Sadaka.
Badaweeyerh Ahmad Mua’zu Jihar Filato:
A ganina abubuwan da suka fi damun al’umma yanzu shi ne; halin tsadar rayuwa da ake ciki musamman ta fannin tsadar abinci da ake fama da shi ba kamar lokutan baya ba, abubuwan na kara faskara da wuce tunanin mai tunani yayin da hakan yake tayar da hankalin mai gida musamman mai iyalai da yawa da mafi yawansu ke cikin tsaka mai wuya, duba da yadda suke shan wahala wajan nemo abin da za a ci yau da kullum.
Abin da yake janyo hakan kuwa laifin gwamnati ne ta hanyar tsawallawa talakawa musamman rashin samar da abinci daga rumbun gwamnati, sanya son zuciya a wajan masu madafun iko wanda idan aka bayar da tallafin abinci a rabama talakawa to abincin baya isa hannun wadanda ya dace su karba, sai dai a kara wa masu karfi karfi wato dai yasu-yasu suke raba kayansu.
Hanyar da za a magance wannan matsalar kuwa hanya ce mai sauki idan gwamnatin da ke da alhakin yin hakan ta so yi, za ta yi amfani da hanyar da ta ke isar da alluran riga-kafi ta hanyar bin talakawanta da mabukata har gidajensu wajan ba su tallafin abincin, domin damar musu cikin saukakakkiyar hanya, ko shirya taro na musamman dan gabatar wa da talakawa wani tallafi kamar yadda suke yi a lokacin yakin neman zabe.
Faisal Salisu Sadau Gama Nasarawa LGA Jihar Kano 07064271220:
Abin da ya fi samun al’umarmu shi ne; yawan ‘yan mata da samari kara zube babu aure. Hakan ya samo asali sakamakon rashin aikin yi da matasan suke fuskanta da kuma tabarbarewar tattalin arziki da mutane ke fama da shi.
Hanya daya ita ce; gwamnati da mahukunta su taimaka domin samarwa matasa aikin yi sannan a kowanne bangare da mata da mazan su rage buri sannan su nemi ilimin addini dana zamani domin gujewa fadawa halaka.
Sunana Sumayya:
Halin da al’umma suke ciki a yanzu shu ne; Talauci, karancin Tattalin Arziki. Abin da ya kawo afkuwar hakan da kuma hanyar magance matsalar ba komai bane face Gwamnati ta sawarwa Matasa Aikin Yi.
Mas’ud Sale Dokadawa:
Rashin ayyunkan yi ga mata matasa da matsakaitan mutane, Rushewar tattalin arziki, gurbatar harkar ilimi, karancin Tarbiyya ga masu tasowa.
Rashin kilowatt gwamnati, karancin cancantattun malamai don koyar da dalibai, halin ko in kula da iyaye ke nunawa kan tarbiyya,raina kananan sana’oi ga matasa.Hadin guiwar gwamnati da al’umar gari kan abin da ya shafi tsaro, farfado da masana’antu don ci gaban kasuwanci, inganta ilimi tun daga tushe, kulawar iyaye kan tarbiyya da ilimantar da ‘ya’yansu.
Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki Jihar Kano:
Gaskiyar magana abin da ya fi damun al’umma shi ne; Talauci, domin kuwa talauci shi ne ke haifar da dukkan wata braka tsakanin al’umma, misali daga lokacin da aka ce ka na da ‘ya budurwa ba za ka iya daukar nauyin karatunta ba da bukatunta, to za ta samu saurayi da zai yi mata hakan, ta wannan hanyar saurayi zai iya lalata maka ‘ya ya rude ta.
Abin da ya janyo hakan bai huce rashin tsoron Allah ba da sakacin shuwagabanni. Hanya daya ce za a maganace hakan shi ne; kowa ya koma ga Allah ya dage da neman gafara ga Ubangiji Allah zai yaye in sha Allah.
Ahmad Hassan (Ahmad dogo Na Salima) Shehu Guarantee oil daga Jihar Kano:
Abin da na fahimta shi ne; abubuwan dake damun al’umma suna da yawa matuka, amma dai abubuwan da suka fi tsanani su ne; Talauci, Rashin tsoro, Talauci kan lalata tarbiyyar yaranmu da zamantakewar al’ummar tare da jefa matasa a shaye-shaye.
Rashin tsoron Allah, Shi ne ya sanya shugabanni zalunci, talakawa kuma su ke yin biyayya da addu’a domin komawa zuwa ga Allah. Abin da janyo hakan sabon Allah, domin sabon Allah shi ne ke haifar da dukkan wata musiba a rayuwa, Mafita ita ce; dukkaninmu mu ji tsoron Allah mu kiyaye dakokinsa dukkan damuwarmu za ta yaye In sha Allah.
Aminu Aliyu Kura (Tecno):
A ganina abin da ya fi damun al’umma a halin yanzu shi ne; Jahilci, domin matsawar mutum bai samu ilimi na addini ba to komai zai iya aikatawa, wanda zai kai sa ga sabon Allah har ya fada cikin musiba da tsadar Rayuwa da talauci.
Abin ya janyo hakan kuwa shi ne; talauci da shugabanninmu suka jefa mu a ciki, kuma tarbiyya da zamantakewar al’ummar da ta gurbace. Hanyar da za a magance hakan shi ne a yaki jahilci a cikin al’umma domin jahilci shi ne; makami mafi muni da ke sanya dan Adam a cikin musiba.
Abdulrrashid Haruna:
A zahiri abin da ya fi damun mai rai a wannan lokacin babu kamar karancin tsaro da kuma abin da ita kanta lafiyar za ta ci, da kuma matsaloli na tattalin arziki da abin da yake neman ya faskara.
Tushen faruwar hakan ni a nazarina hakan ya samo asali ne daga shuwagabanninmu a yau, so da dama muna da hujjar kuka da su akan rashin tsaro, da kuma karancin abin da ma za mu ci a yau, sannan da tattalin arzikinmu da ya rushe nauyi ne da yake na su amman sun kasa saukewa sabida haka sune mafari, Hanyoyin magance matsalolinmu a yau, abu na fari shi ne; a inganta tsaro dan kare lafiyar mu, sannan a bude ma’aikatu dan rage zaman banza kasuwanci shima a dago da darajar sa da tayi kasa a yau, sannan ilimi a dawo da kimar sa domin shi ne hasken rayuwa.
Abba Abubakar Yakubu, Shugaban kungiyar Jos Writers Club daga Jihar Filato:
Babu shakka babu abin da ya fi daukar hankali a wannan zamani kamar tsadar rayuwa, musamman yadda kayan masarufi da sauran muhimman bukatun rayuwa suke kara tashin gwauron zabi.
Kusan kullum mutum ya shiga kasuwa ko ya je sayayya a kantunan sayar da kayayyaki, sai ya ji sabon farashi. Ban da tsadar rayuwa akwai matsalar karancin kudi a hannun mutane, hakan ya sa rayuwa ta kara tsada, domin yayin da ake tunanin abin da za a ci, akwai wasu sauran bukatu na yau da gobe, da suka hada da matsalar kula da lafiya, makarantar yara ga masu iyali, zirga-zirga da abubuwan da dan Adam ke bukata don inganta rayuwar sa.
Damuwoyin da suke kan ýan kasa sun fi karfin dan abin da suke samu. Daga cikin dalilan da za a iya cewa sun kawo wannan al’amari akwai tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnati, rufe iyakokin kasa da aka yi, domin hana shigowa da wasu kayayyaki cikin kasa ya taimaka wajen kara farashin abin da ake iya samu na cikin gida, sannan uwa uba annobar Korona da aka fuskanta a farkon shekarar da ta gabata ta haddasa rufe manyan cibiyoyin kudi na duniya da durkusar da harkokin kasuwanci na kasashe.
A dalilin haka tattalin arzikin kasashen duniya, da Nijeriya ke hulda da su, ya samu matsala, hakan kuma ya shafi tattalin arzikin Najeriya da rayuwar jama’ar ta.
A ra’ayina da fahimta ta kan wannan matsala da ta addabi rayuwar ‘Yan Nijeriya, za a iya samun saukin wannan abu ne idan gwamnatin tarayya da ta jihohi za su bullo da wasu dokoki ko tsare-tsare da za su saukaka halin kuncin da ake ciki, ta hanyar rage harajin da ake karba a wajen ‘yan kasuwa da masu masana’antu, rage yawan kudaden da manyan jami’an gwamnati ke ware wa kansu a matsayin albashi ko kudaden gudanarwa, bude iyakokin kasa, da dage takunkumin da ta sanya kan wasu kayayyakin masarufi da aka hana shigo da su, don su taimaka wajen rage farashin wasu kayayyakin da ake kukan tsadar su a kasuwanni.
Yakubu Obida Farawa Ungogo LGA Jihar Kano:
Abin da yafi damun al’umma a wannan lokacin suna da yawa amma na 1 dai talauci ne. Abin da ya janyo afkuwar hakan rashin abun yi ne mutum ya tashi da safe babu inda zai je babu sana’a so komai zai iya faruwa amma in mutum na da sana’a da zai je ya ba da lokacinsa akai ya sami taro da sisi to amma sai aka Sami akasin hakan to kuwa komai zai iya faruwa. Hanyar da za mu iya magance matsalar shi ne; mu yi nesa da duk abin da ke ci mana tuwo a kwarya, mu yi nesa da dukkanin abin da zai bata mana rai, sannan kowa ya nemi abun yi ya tsaya da kafafunsa.