Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce, dakarunta sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP 139, tare da kama wasu 132 da ke bai wa ‘yan ta’addan bayanan sirri, sannan kuma ta kubutar da mutum 60 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa dasu a makonni biyu da suka gabata.
Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, wanda ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a rahoton mako-biyu da rundunar ke fitar a tsakanin 6 zuwa 20 ga watan Oktoba, 2022, ya ce ‘yan ta’addan Boko Haram 366 da iyalansu sun mika wuya ga gwamnatin jihar Borno, sannan kuma shugabannin ‘yan bindiga biyu da mambobin su dake Jihar Zamfara, su ma sun mika wuya ga gwamnatin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar sojojin ta Operation Hadin Kai a lokacin da take binciken sirri, ta kama mutum 72 masu samar wa ‘yan ta’adda da makamai, sannan ta kashe 49 daga cikinsu.
Ya bayyana cewa, sojoji a ranar 11 ga Oktoba, 2022 sun fatattaki ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP, a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’addan suka kai a kauyen Gala Kura da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Daraktan ya ce an kashe ‘yan ta’addar Boko Haram guda daya a arangamar tare da kwato bindigogin AK47 guda biyu.