Wadannan sune jerin garuruwa guda 10 wadanda suke da dadin ziyarta a duniya, idan ka na da kudi kuma ka na sha’awar zuwa yawon bude ido ko shakatawa, sannan kana taraddadin rashin sanin ina ne zaka nufa, a wannan makon ina dauke ne da jerin wasu garuruwa 10 da suke kan gaba wurin zaman lafiya, sauki da dadin ziyarta a fadin duniya.
A sau da yawa za ka ga mutum ya tara kudi, yana bukatar hutawa da nishadi, amma bai san daga ina zai fara ba, don haka ne na lalubo wadannan wurare domin su zama mabudin ido ga wadanda ke da hali.
Shi hutawa da nishadi, musamman ga wadanda ke da Iyali kuma suke da hali, ya na kara dankon soyayya a tsakanin masoya da kuma fahimtar juna. Sannan ziyartar wuraren shakatawa na cire wa mutum wasu ‘yan damuwowin dake addabarsa, walau a wurin aiki, ko kuma a tsakaninsa da abokan sana’a ko cinikayya.
Kowanne wuri a cikin jerin guda 10 din nan, yana da nashi abin burgewa da jan hankali. wuraren sune kamar haka:
GARIN ANTELOPE CANYON, USA
Garin Antelope ya kawatu da wani tafkeken magudanan ruwa a Nabajo, wanda ke gudana a tsakanin wasu tsaunuka, abin gunin ban sha’awa. Wannan na daga cikin abubuwan da suke janyo hankali masu zuwa yawon bude ido da shakatawa zuwa garin. Haka kuma garin na da tarihin zaman lafiya, babu tashe – tashen hankula.
GARIN ICE CABE, ICELAND
Gari ne da a ke kankara, sannan kuma akwai wadatar ruwan sama, da zaran an yi ruwan sai dusar kankara ta daskarar da shi, wanda ke sa garin ya dau sanyi. Duk da haka sanyin bai zama mai tsananin gaske, wanda ya na daga cikin abubuwan da ke janyo hankalin maziyarta, tare kuma da zaman lafiya da kwanciyan hankalin da a ke da shi a garin.
TSIBIRIN GLASS DAKE CALIFORNIA
A yankin Fort Bragg da ke garin California ne mutum zai tarad da abubuwan al’ada masu ban sha’awa iri – iri. A wani tsibiri da a ke kira da tsibirin ‘Glass’, a tsibirin akwai duwatsu masu nau’in gilashi, wanda ba a bari maziyarta su diba, sai dai su shakata sannan su samu karin ilmi. Mutane na tururuwa zuwa wannan wuri musamman a lokutan hotun karshen shekara. Haka kuma a karshen watan Mayun kowacce shekarar a na gudanar da wani gagarumin buki a tsibirin wanda a ke kira da bukin gilashi.
ZHANGYE DANDIA, CHINA
A yankin Gansu na kasar China, akwai wani wurin shakatawa mai suna Zhangye Dandia wanda ya shahara a gaba daya lardin Asiya, an kawata wurin da ado na musamman. Akwai tsaunuka masu ban sha’awa a wannan wurin shakatawa, wadanda ke kara girma lokaci bayan lokaci. Hukumar UNESCO ta ambaci wannan wuri da cewa ya na daga cikin jerin wuraren da su ka fi jan hankalin maziyarta a duniya.
MASHIGIN SOYAYYA DAKE UKRAINE
A wani daji a garin Ukraine, an samar da wani kawataccen wurin yakkon bude ido da shakatawa ga maziyarta a karkashin kasa, wanda a ka yiwa lakabi da mashigin soyayya. Wurin ya na da tazarar kilomita 24 tsakaninshi da garin Ribne na birnin Kleban. A wannan mashigi na karkashin kasa akwai bishiyoyi da filawowi wadanda su ka yalwata wurin . yawancin wadanda su ka fi ziyartan wurin daga masoya sai ma’aurata, domin yadda a ka tsara wurin an yi shi ne musamman don kara dankon soyayya a tsakani. Ma’aurata kan ziyarci wurin domin su yi hotuna, haka nan ma masoyan juna, saboda wuri ne da bayar da daman yin hotuna masu kyawun gaske.
WURIN SHAKATAWA NA ‘GIANT’S CAUSEWAY’, IRELAND TA AREWA
A hasashe a na cewa wannan wurin shakatawa na ‘giant’s causeway’ da ke wani tsibiri a kasar Ireland ta Arewa ya samu ne sama da shekaru miliyan 50 da su ka gabata, sannan duk abubuwan tarihi da ke wurin suna nan ne tun daga wadancan shekarun. Wuri ne da maziyarta ke yawan ziyarta lokaci bayan lokaci.
NAICA MINE, MEDICO
A shekarar 2000 ne a ka gano wannan wurin, tsibiri ne wanda ke da fadin da ya kai girman filin kwallon kafa, sannan kuma tsayinsa ya kai na dogon gini mai hawa biyu. Idan ka na burin ziyartan wannan wurin shakatawa, ka shirya da kayan sanyinka, saboda a kan yi sanyi mai tsanani a wasu lokuta a wurin.
RED BEACH, CHINA
Wurin babban wurin shakatawa na bakin teku ya na a garin Panjin ne da ke kasar China, ya na dauke da wani tsibiri wanda ke sauya launi zuwa kore daga watan Afrilu zuwa wani lokaci. Daga nan kuma ya kan sauya zuwa jajur bayan lokaci mai tsawo. Mutane na son zuwa yawon bude ido da shakatawa a wanan wuri don ganin ikon Allah.
SALAR DE UYUNI, BOLIBIA
Idan ka na tantaman wurin da za ka samu wurin shakatawa mai gamsarwa a duniya, ka jaraba zuwa Salar du Uyuni, shi ne wurin da ya fi ko ina yawan kasa mai gishiri, saboda tekunan da ke jone da garin. Akwai zaman lafiya da kwanciyan hankali.
“KOFOFIN WUTA”, TURKMENISTAN
A dajin Karakum na Turkeministan akwai wani wuri mai tsawon mita 70 wanda a ke kira da ‘kofofin wuta’. An ce wani masananin yanayi ne na kasar Sabiya ya samar da wurin a shekarar 1971, wanda a ka samu fashewar wani abu wuta ta kama, tun daga wancan lokacin wutar ta ke ciki har zuwa yau. Don haka ne a ka zagaye wurin mutane na zuwa yawon bude ido da shakatawa, tare da ganin ikon Allah.