Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya kokakan halin da malaman jami’o’in gwamnati ke ciki dangane da komawa ajujuwa bayan dakatar da yajin aikin da ya kwashe watanni takwas ana yi.
Gwamnati dai a lokacin yajin aikin ta hana malaman albashi a bisa tsarin “Babu aiki ba biyan albashi.”
- Ba Mu Taba Ganin Ambaliyar Ruwa Mafi Muni A Nijeriya Kamar Ta Bana Ba – Gwamnati
- Xi Ya Jaddada Aiwatar Da Muhimman Ka’idojin Babban Taron JKS A Cikin Rundunar Sojojin Kasar
A wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels TB, Osodeke, ya ce an dakatar da yajin aikin ne bisa bin doka duk da babu wata yarjejeniya da aka rattaba hannu a kai tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
“Kamar yadda kuke gani daga sanarwar da muka fitar na dakatar da yajin aikin, mun bi umarnin kotu ne, mu kungiya ce masu bin doka da oda ba tare da a sanya hannu kan wata yarjejeniya ba. Muna fatan shiga tsakani na kakakin majalisar wakilai ya yi zai zama wata sila ta warware dukkan batutuwan kamar yadda yakamata.”Ta yaya mambobin za su yifarin ciki yayin da aka tilastamusu komawa bakin aiki ba tare da an warware matsalolin kuma an biya bukatunsu ba?
Mafi kyawun zabi don warware batutuwa irin wannan shi ne, tattaunawa, amma ba a yi hakan ba. Muna da yakinin ‘yan uwa za su je su koyar, amma ta yaya mutumin da yake zaune da yunwa kuma ba shi da yadda zai yi, sannan bankuna na bin sa bashi saboda rashin albashi zai samu sukunin gudanar da aikin koyar da wani abu,” in ji shi.