A kwanakin baya, ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta gabatar da rahoton binciken yanayin amfani da makaman nukiliya na shekarar 2022 wato NPR a takaice, game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, wannan rahoto ya fadakar da ra’ayin takara a tsakanin manyan kasashe ko kungiyoyi, da maida makaman nukiliya a matsayin abin sa kaimi ga yada ra’ayin siyasa bisa yanayin wuri, abun da ya sabawa ra’ayin hana yakin makamashin nukiliya da gasar ajiye makaman nukiliya da kasa da kasa suka amince da shi. A don haka, kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta yi watsi da ra’ayin yakin cacar baka da manufar kama karya, da daukar matakan dake shafar makaman nukiliya masu dacewa, da sauke nauyin dake wuyanta na rage makaman nukiliya don taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp