ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Kula Da Fatar Jiki (4)

by Bilkisu Tijjani
4 years ago
Fatar Jiki

Busasshiyar Fata: Za ki iya gane busasshiyar fata ce da ke ta hanyar wadannan alamu: Saurin bushewar fata a lokacin iska ko dari, yawan yi saba, kyasbi, fashewan lebe a lokacin iska ko dari, yawan jin kaikayi da kasancewar fata ta yi fururu kamar an bada miki garin fulawa, yamutsewar fata da sauransu.

Ko shakka babu irin wannan fatar ta fi kowace irin fata bukatar gyara, kuma wannan darasi ya zo miki da hanyoyin magance matsalar bushewar fata.

  • Kasar Sin Ta Jinjinawa Hanyoyin Da Kasashen Yankin Manyan Tafkunan Afirka Ke Bi Wajen Magance Matsalolinsu
  • Xi Ya Taya Murnar Shirya Bikin Liyafar Shekara-Shekara Ta Kwamitin Huldar Amurka Da Sin

Ga Hanyoyin Magance Matsalar Bushewar Fatarki:

ADVERTISEMENT

Daina wanka da ruwa mai zafi domin yana taimakawa wajen tatse maikon da ya saura gareki ki daina zama a cikin rana mai zafi kayan sawarki ya kasance mai laushi ba mai gautsi ba, sannan ki daina yawan barin jikinki ko wani bangare na jikinki a bayyane musammam a lokacin iska Lebenki ya kasance a koda yaushe ya kasance cikin mai ko da basilin ko lip gloss mara kala.

Ki kiyayi jambaki na wani dan lokaci ko kuma daga kin gama abin da za ki yi da Jambakin ki goge ki sa lip gloss dinki idan za ki yi burushi da safe ki wanke har da labbanki domin za su yi laushi kuma matacciyar fatar leben zai fita.

LABARAI MASU NASABA

Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi

A Matsayinki Na Mace, Kada Ki Yi Wasa Da Wadannan Abubuwa

Sai dai ba a goga burushin da karfin tsiya ki dinga yawan shafa madarar yoghurt a fuskarki ko madara idan ta bushe, sai ki dauraye da ruwan sanyi sosai kada ki rika yawan durje fuskarki kuma kada ki yawaita amfani da Sabulu da yawa ki rika yawan amafani da mayuka da aka yi su da dan itaciyyar APRICOT ko kuma ya kasance da akwai shi a ciki musamman ma ga kanki ki sayi OATS ki nika shi ya yi laushi sosai idan za ki yi wanka sai ki debi cokali daya ki zuba a kofi daya na ruwan zafi ki juya idan ya narke sosai sai ki zuba a ruwan wankanki juya da kyau (ruwan wankanki ya zama shi ba mai sanyi ba kuma ba mai dumi ba. Idan kin gama kada ki goge jikinki ki bari fatarki ta shanye ruwan jikin naki.

Abocado (piya) ki cire bawon kiyar sai ki dama ta yi laushi ki shafe ta a fuskar (kina lailaya fuskarki a hankali) idan ya bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi sosai ki raba ruwan wankan ki biyu, idan kin gama wanka da daya sai ki shafa basilin (baseline) ko man kade sannan ki watsa sauran ruwan a jikinki.

Za ki sake shafa mai in kin fito ki yawaita shafa wa fuskar ki da hannu da kafarki mai duk bayan kowace Sallah domin sun fi komai bushewa a jikinki, idan za kishafa mai a fuskarki, bayan kin lakato man a hannunki kin mutsuttsika sai ki fara tafa hannunki duk biyun akan fuskarki a hankali ko ta ina har sai man ya shafu a haka.

Kwalliya A Lokacin Zafi: Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da black heads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.

Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi: Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko.

A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.

Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya ba cewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.

Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kalamai haske.

Kada kuma a manta shafa hoda mai haske akan hanci. A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.

Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.

Yadda Ake Kwalliyar Fuska Mata da dama musamman ma wadanda za su yi aure su kan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska.

Babu shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyar za a iyayin ta a gida idan akwai kayan aiki. Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ta bushe kafin a shafa mata komai.

Ana so a samu ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga. Bayan an yi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula). A samu hodar fandesho dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.

A samu hoda haka a sake shafawa. Sannan sai a samu reza ga wanda ke da cikar gira sai aske ta kadan. A samu gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana girar da shi.

Bayan haka sai a samu ‘concealer’ da na ‘eye shadow’da burushin ‘eco tools’ da burushin ‘eyeliner’. Sai a fara taje giran da burushin ‘eyeliner.’

Sannan saia zana girar da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hada su. Bayan an shafa sai a sake taje su da ‘eyeliner brush’din.

Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a girar. A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.

A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum. Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za asaka. Sai a shafa janbaki. Shi ke nan kwalliya ta kammala.

Mun ciro daga shafin Ado Da Kwalliya Online

Fatar Jiki
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji

MASU ALAKA

Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi
Ado Da Kwalliya

Hanyoyin Hada Humra Mai Kamshi

June 14, 2026
A Matsayinki Na Mace, Kada Ki Yi Wasa Da Wadannan Abubuwa
Ado Da Kwalliya

A Matsayinki Na Mace, Kada Ki Yi Wasa Da Wadannan Abubuwa

June 6, 2026
Ko Kin San… Cututtukan Da Man Ridi Ke Warkarwa?
Ado Da Kwalliya

Ko Kin San… Cututtukan Da Man Ridi Ke Warkarwa?

May 17, 2026
Next Post
Zamanintarwa Irin Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Shimfida Zaman lafiya Da Kwanciyar Hankalin Duniya

Zamanintarwa Irin Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Shimfida Zaman lafiya Da Kwanciyar Hankalin Duniya

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Gurfanar Da Tubabbun ’Yan ta’addan Da Suka Sake Aikata Manyan Laifuka

July 14, 2026
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Kyawawan Manufofin Buhari Za Su Ci Gaba Da Yi Wa ’Yan Nijeriya Tasiri – Tinubu

July 14, 2026
Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

Abin Da Ake Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin” Da Aka Yanke Wa Sin Na Kashin Kanta Ba Shi Da Wani Amfani

July 13, 2026
Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

Tafiye-tafiyen Fasinjojin Jirgin Kasa A Kasar Sin Sun Haura Biliyan 2.3 A Rabin Farko Na Bana

July 13, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙaddamar Da Tsarin Daƙile Rugujewar Gine-Gine

July 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.