Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu nasarar cafke hakimin kauyen Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Abubakar Ibrahim, bisa zarginsa da shiga hada-hadar miyagun kwayoyi.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce, Basaraken na daga cikin mutum goma sha daya da aka kama bisa zargin hada-hadar kwaya 991,320 na maganin opioids da kuma Wiwi mai nauyin kilograms 1,251 da kuma Khat hadi da kilograms 46.637 na Methamphetamin, Cocaine da Heroin wadanda hukumar ta kamo a jihohi shida.
A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba a filin sauka da tashi na Jirgin saman Murtala Muhammad da ke Ikeja Legas, jami’an NDLEA masu kula da hidimar shigo da kayayyaki da ke aiki a SAHCO sun kama katan guda 15 dauke da Kwayoyin tramadol 802,000 da aka shigo da su daga kasashen Dubai, UAE da kuma Karachi, Pakistan.
Dukka a wannan ranar, jami’an sun kuma cafke gwangwanin tumatur da aka shirya kaiwa Ingila.
Hukumar ta ce, bisa zurfafa bincike sun gano cewa gwangwanin Tumatur din an yi amfani da su wajen boye kwalayen tabar Wiwi 36 masu nauyin kilogirams 21.30 kuma jami’in dakon kayan mai suna Sodehinde Akinwale shi ma an kama shi tare da kayan.
Kwanaki biyu bayan nan, jami’an hukumar da ke aiki tare da NAHCO masu kula da shigo da kaya a filin Jirgin Legas suka cafke katan biyar na busasshen Khat mai nauyin kilograms 107.70 da suka taho daga Bangkok da ke Thailand ta Dubai a Jirgin Emirates.
Kazalika, jami’an hukumar sun cafke wani matashi mai shekara 27 Madu Chukwuemeka Miracle a filin Jirgin saman kasa da kasa ta Akanu Ibiam, AIIA, Enugu bayan dawowarsa daga Nairobi, Kenya ta Addis Ababa, Ethiopia a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba.
Da aka bincike kayansa an kama shi da kodin da dama.